Daga cikin abubuwan da za ayi na bukukuwan cika shekara 50 da kafa Jami’ar Ilori,kami’ar zata karrama mashahuran ‘yan Nijeriya 65 ranar Laraba ta wannan makon da muke ciki.
Tsarin bikin da aka yi ma taken,: “Karrama wasu mashahuran mutane wadanda suka kasance masu taimakawa jami’ar ne,da kuma wadanda suka halarci makarantar, babbar karramawar da za ayi ta nuna, sanin ana yin abubuwa ko ayyuyka masu nagarta da suke kawo ci gaba,” za ayi hakan ne da karfe 11:00 na safe a dakin taro na jami’ar.
- ‘Yansanda Sun Hana Gudanar Da Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Obi A Kaduna
- Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa
Sanarwar data fito daga ofishin darekta na al’amuran hulda da mutane na jami’ar,Mista Kunle Akogun,ta samu bayanai daga Shugaban kwamitin shirya karramawar, Farfesa AbdulRasheed Adeoye, yana cewa“ bikin zai karrama wadanda suka halarci jami’ar da kuma wadansu mutane, da suka samu nasarori, a wuraren da suke aiki ko suka yi suka kuma bada tasu gudunmawa wajen ci gaban jami’ar da al’umma.’
Bayanin ya kara da cewa,“daya daga cikin wadanda suka halarci jami’ar, da kuma wani mashahurin mutum dan Nijeriya za su samu karramawar data fi ko wace, akwai ma wasu, mutane 10, da za a karrama su da sunan matsayin wadanda suka yi jami’ar suma sun yi manyan abubuwan,da suka dace,sai kuma wasu mutane 50 da kuma,3 daga cikin wadanda za’ a yaye,su za a karrama su da nambar ‘Jakadun jami’ar Ilori.”
Kamar yadda Shugaban kwamitin yace,” Shi bikin ba wai kawai abin ya tsaya bane kan nasarorin da suka samu bane wadanda za a karramawar, saboda wani lokaci ne da za a yi tunanin baya ga mu wadanda suka halarci jami’ar Ilori inda muka zama ‘ya’uwa daya.”
Wadanda za ayi ma,karramawar sun,hada da mataimakin Shugaban jami’ar na 8,da kuma rajistara na Hukumar shirya jarabawar shiga manya makarantu (JAMB) Farfesa, Emeritus Is’hak Oloyede,Dakta Tunji Olowolafe, Dakta Adeyemi Adeniji,mataimakin Shugaban jami’ar fasaha ta tarayya, Akure (FUTA), Farfesa Temidayo Oladiji; sai tsohon Shugaban Hukumar kula da lamuran iskar gas ta kasa Mista Babatunde Omotowa; babban kuma sanannen Akanta, Dakta AWA Ibrahim; tsohon mataimakin gwamnan Babban Banki na kasa, Dakta Sarah Alade; Komfuturola Janar ta Hukumar shige da fuci ta kasa, Mrs Kemi Nandap; da kuma Shugaban Jaridar THISDAY, Mista Eniola Bello da dai sauran makamantansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp