Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya gargadi kungiyoyin da ke shirin shiga zanga-zanga da su guji tada tarzoma.
Wannan na zuwa ne gabanin zanga-zangar da kungiyoyin kwadagon Nijeriya NLC da TUC suka shirya yi a fadin kasar a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023.
- Da Dumi-Dumi: Jirgin Sama Ya Yi Hatsari A Legas
- Bana Iya Barci Saboda Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki -Tinubu
Kakakin hukumar, ACP Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce IGP ya damu matuka game da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan game da zanga-zangar da kungiyoyin kwadagon Nijeriya (NLC) da ma’aikata (TUC) suka shirya yi a fadin kasar.
“Duk da haka, IGP ya amince da korafe-korafen da kungiyoyin kwadago suka gabatar, wanda bai dace ba, wajen magance wadannan batutuwa.”
“Bisa la’akari da kalubalen da ke tattare da shirin gudanar da zanga-zangar, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta shirya tsaf don tura duk wani abu da ake da shi domin tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar.
“Shugaban ‘yan sandan ya bukaci masu ruwa da tsaki da suka hada da NLC, TUC, da sauran kungiyoyin farar hula da su rungumi zaman lafiya a matsayin hanya mafi inganci don warware korafe-korafe, tare da jaddada cewa ‘yan sanda sun dukufa wajen ganin an samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali.”
Saboda haka, ya kara da cewa Sufeton ya umarci kwamishinonin ‘yan sanda da masu kula da zaman lafiya.
Ya nanata kudurin rundunar ‘yan sandan Nijeriya na tabbatar da tsaro da tsaron dukkan ‘yan kasa a lokacin gudanar da zanga-zangar da aka shirya yi.