Connect with us

LABARAI

Abin Da Ya Sa Buhari Ke Tsoron Zaben 2019 – PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP ta ce, shelantawar da Shugaba Buhari ya yi na cewa, Jam’iyyar APC kadai ba za ta iya da adawar da ke gabanta ba gabanin babban zaben 2019, wannan aminta ne da cewa ba shi da goyon bayan da ya samu a lokacin da aka zabe shi a 2015.

Jam’iyyar ta PDP ta fadi hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi ta hannun Sakatarenta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, inda ya ce, tsoron da Jam’iyyar ta APC da kuma Shugaba Buhari suke da shi, ya taso ne daga gazawar da suka yi na cika alkawurran da suka yi a lokacin yakin neman zabe ga al’ummar Nijeriya.

“Abin takaici ne yadda Shugaban kasan ke kokarin nade tabarmar kunya da hauka, shafa wa mutane bakin fenti da kuma sukan Jam’iyyar PDP, a maimakon ya amsa gazawar da ya yi na cikawa al’umma alkawurran da ya yi masu a lokacin yakin neman zabe.
Advertisement

labarai