Wasu manoman Rogo a kasar nan na fuskantar kalubalen samun ingantaccen tushen Rogon da za su shuka a gonakan su, musamman domin su samu yin girbi mai dimbin yawa kari da rashin samun kayan aiki na zamani daga daga gun gwambatin tarayya da na jihohin da ke a kasar nan.
Har ila yau, manoman sun kama fuskanci kalubalen wadatacciyar kasar yin noma da rashin gyran kasar noman da rashin kayan noma na zamani da rashin wadatattun kudaden yin noman da sauransu.
- Bukatar Magidanta Su Sa Ido Kan Yadda ‘Ya’yansu Za Su Yi Bikin Sallah
- Yadda Kamfanin Huawei Na Sin Ke Fadada Moriyar Fasahar Sadarwa A Tanzania
Sai dai, duk da irin wadannan kalubalen, manoman Rogo a jihar Edo na cike da murna, musamman wajen samun yin girbi mai yawa daga Rogon da suka shuka, inda hakan ya kai jihar a matsayi na Gaba, wajen samar da Rogon mai dimbin yawa.
Shugaban kungiyar manoman Rogo da sarrafa shi zuwa Garin Rogo a jihar ta Edo Donatus Imaghodor ya bayyana cewa, har yanzu manoman na Rogon a jihar samun karin ci gaba a nomansa duk da irin wadannan kalubalen da ake samu wajen yin nomansa.
A cewar shugaban, akasarin e fuskanta a jihar ta Edo shine karancin kasar yin noma bane yawan samun gobara da rashin wadatattun kudaden da rashin kayan aiki na zamani da sauransu. Imaghodor ya bayyana cewa, zai fi yiwa manoman a jihar sa  sauki idan sun samu kayan nomansa na zamani aiki sa.
Ya kara da cewa, manoman sa na fuskantar kalubalen samun kayan nomansa na zamani duk da cewa, suna samun wadataccen tushensa da ake shukawa sai kuma gobara ta auka a cikin wasu gonakan da manoman sa ke shuka shi.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa, akasarin manoman sa na sa samun magungunan yi masa feshi, musamman don dakile yaduwar Ciyawa a cikin gonakan da aka shuka shi, inda ya bayyana cewa, babu kuma wani tallafi da ke zuwa ga manoman daga gun gwamnatin jihar.
Sai dai, Imaghodor ya sanar da cewa, a wasu lokutan ta hanyar shirin bunkasa aikin noma na jihar ADP manoman sukan samu taimako da wasu kayan aiki wadanda kuma ba sa isar manoman na Rogon da ke a cikin jihar.
Ya bayyana cewaz har zuwa yanzu, manoman na Rogon a jihar mun yi sa’ a a yanzu, bamu fuskanci kalubalen rashin tsaro ba, musamman rikicin manoma da Fulani Makiyaya.
” Mun yi sa’ a a yanzu, bamu fuskanci kalubalen rashin tsaro ba, musamman rikicin manoma da Fulani Makiyaya. “
A cewar Imaghodor, idan manoman na Rogon ba su da kayan aikin ma zamani, za su iya fara yin noman dan kadan, inda ya ce, zai fito ya farawa da noma kadada 100.
Shugaban ya bayyana cewa, ga duk wanda sabo ne zai shiga fannin na noman Rogon dole ne ya ce tabbatar da ya samu gona tukunna da kudi da kayan aiki na zamani.
“Idan manoman na Rogon ba su da kayan aikin ma zamani, za su iya fara yin noman dan kadan, inda ya ce, zai fito ya farawa da noma kadada 100.’