ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Yake Kashe Matanmu Na Hausawa

by Bilkisu Tijjani
3 months ago

Mene ne dalilin da yasa Matan Hausawa suke saurin tsufa da zaren an yi musu aure sun je gidan miji. Zaka ga yarinya ƙarama wacce aka haifeta a gabanka da zaren ta isa aure an kaita ɗakin miji shekara ɗaya kawai zuwa biyu bayan ta haihu idan ka ganta abin zai baka tsoro da mamaki domin zaka ganta duk ta tsufa ta yanƙwane kamar wata gwaggwo

Abin da yake bani mamaki shi ne kafin ƴan matan su yi aure sun iya kama jikinsu da ɗaukar wanka da kwalliya. Watakila wannan shi ne dalilin da ya sa samari suka yi mata chah a lokacin tana gidansu. Amma da zaran ta shiga ɗakin miji shikenan wannan kama jikin da wannan wankan da kwalliya duka sun zama tarihi.

Musamman idan ta samu juna biyu ko kuma ta haihu a wannan lokacin wata matar ko abincin da ta dafa wani namijin mai ƙyanƙyami ba zai iya ci ba balle har ya yi hira ko haɗa shimfiɗa da ita ba. Kuma a irin wannan yanayin ba kowane namiji ba ne zai iya zama da irin waɗannan matan ba dole sai dai cikin biyu a yi ɗaya ko dai ya saketa ko kuma ya ƙaro aure.

ADVERTISEMENT

Da yawa matanmu haka suke basu damu da ado da gyaran jikinsu ba kamar yadda suke a lokacin suna ƴan mata. Dalilin kenan da ya sa mazajensu ke gudunsu suna bin ƴan matan waje ko karuwai. Domin matansu basu yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen ƴan matan waje.

Kullum zaka tarar da mace da ɗaurin ƙirji kai a chukurkuɗe ya tsufa ba kitso ba gyara. Yadda take a hargitse haka ‘yaƴanta da ɗakinta da gidanta suke babu kulawa. Idan mijin ya yi magana domin ta gyara sai ta ce:

LABARAI MASU NASABA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

“Kawai dai Baban wane ka gaji da ni ne duk shi yasa kake ta yimin irin wannan tsangwamar. To ya kake son na yi ni inji ce da zanyi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa na yi wanka kuma na share ɗakin nan sannan na yi wa yaran nan wanka”.

Babu yadda mijin ya iya dole sai dai ya yi haƙuri ya daina gayyato abokansa gidan don kada su fahimci matsalar matarsa ko kuma ya fara tunanin sakinta ko ƙara aure.

Abin da zai baka mamaki shi ne irin waɗannan ƙazaman matan idan suka tashi fita unguwa wallahi idan ka gansu ba zaka iya ganesu ba. Wanka suke ɗauka a yi kitso da ƙunshi da gyaran jiki kamar za ta gasar kyawawa. Har ƙananen ‘yaƴansu sun ganesu da zaren sun yi kwalliya to unguwa za a tafi sai ka ga yaran sun fara binsu suna yi musu kuka don kada iyayen su tafi su barsu a gida.

Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)
Uwargida Sarautar Mata

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Next Post
Obi Ya Zaɓi Kwankwaso A Matsayin Abokin Takararsa

Obi Ya Zaɓi Kwankwaso A Matsayin Abokin Takararsa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.