ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

by Sulaiman
2 hours ago
Uwargida

Kishi wani yanayi ne da ke tasowa a zuciyar mutum sakamakon cakuɗuwar fushi, hassada, ƙyashi da ƙin yarda da shiga cikin abin da yake ganin nasa ne. Wannan yanayi kan bayyana ne idan mutum ya ji cewa wani yana son shiga huruminsa ko kuma ya yi tarayya da shi a abin da yake so ko ya mallaka.

Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallam ya sanar da mu cewa Allah Maɗaukakin Sarki yana da kishin da ya dace da Shi, haka kuma ya halicci bayinsa da kishi a cikin ɗabi’unsu. Sai dai Allah shi ne mafificin masu kishi.

Kishi ya kasu gida biyu:

ADVERTISEMENT

1. Kishi mai kyau:

Kishi mai kyau shi ne wanda mutum yake iya sarrafa zuciyarsa da kuma hana ta bin son rai. A lokacin da hassada, ƙeta ko ƙyashi suka taso, sai yayi ƙoƙarin danne su, maimakon ya bari su rinjaye shi. Irin wannan kishi kan sa mutum ya yi burin samun irin alherin da wani yake da shi ba tare da ya yi masa hassada ko ya yi fatan ya rasa abin ba. Haka kuma yana taimaka wa mutum ya kula da abin da yake so ba tare da son mallake shi shi kaɗai ba, musamman idan abin yana da masu tarayya da shi, kamar miji a tsarin aure. Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallam ya ce:

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Yake Kashe Matanmu Na Hausawa

Kafin Ki Nemi Saki, Nemi Amsar Waɗannan Tambayoyi Da Kanki

“Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai ya so wa ɗan’uwansa abin da yake so wa kansa.”

Kishi marar kyau:

Kishi marar kyau kuwa shi ne wanda hassada, ƙeta da ƙyashi suka mamaye zuciya har mutum ya kasa sarrafa kansa. Wannan ne ke haifar da zafin kishi wanda wani lokaci kan kai ga aikata munanan ɗabi’u da ayyuka. A wannan rubutu, za mu yi bayani ne kan wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa zafin kishi a cikin al’umma.

Dalilan da ke haddasa zafin kishi:

1. Rashin kyakkyawar tarbiyya tun Ƙuruciya:

Wasu lokuta matsalar zafin kishi ta samo asali ne daga irin tarbiyyar da yarinya ta samu tun tana ƙarama. Akwai iyaye mata da ke cusa wa ƴaƴansu tun suna yara cewa kishiya abokiyar gaba ce, suna kuma nuna musu hakan ta hanyar munanan kalamai ko mummunar mu’amala da abokan zamansu. Idan irin wannan tunani ya ginu a zuciyar yarinya tun tana ƙarama, ilimin boko ko na addini kaɗai ba zai wadatar wajen kawar da shi ba matuƙar ba a gyara tushen matsalar ba.

2. Rashin haɗa Ilimi da Tarbiyya

A wasu makarantu ana mayar da hankali ne kan koyar da ilimi kawai, ba tare da ba da muhimmanci ga tarbiyya ba. Wannan ne ya sa wani lokaci mutum zai kasance mai ilimi amma ba shi da kyawawan ɗabi’u. A da, malamai suna haɗa ilimi da tarbiyya, abin da ya taimaka wajen gina mutanen kirki a cikin al’umma.

3. Wasu kurakuran mazaje:

Wasu mazan kan yi alkawurran da ba su da tabbacin cika su, musamman kafin aure. Wasu kan yi wa mace alkawarin cewa ba za su ƙara aure ba, sannan daga baya su canja ra’ayi.

Irin wannan yanayi kan haifar da rashin jituwa da fitina a gida, musamman idan an gina aure ne a kan abin da ba zai yiwu a tabbatar da shi ba.

4. Rashin Adalci Tsakanin Mata:

Rashin adalci tsakanin mata na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa fitina a gidajen aure. Idan mace ta ji ana nuna son kai ko ana tauye mata hakkinta, hakan kan haddasa bacin rai da rikice-rikice.

Uwargida
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi
  • Sulaiman
    An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam
  • Sulaiman
    Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

MASU ALAKA

Abin Da Yake Kashe Matanmu Na Hausawa
Uwargida Sarautar Mata

Abin Da Yake Kashe Matanmu Na Hausawa

May 30, 2026
Kafin Ki Nemi Saki, Nemi Amsar Waɗannan Tambayoyi Da Kanki
Uwargida Sarautar Mata

Kafin Ki Nemi Saki, Nemi Amsar Waɗannan Tambayoyi Da Kanki

May 24, 2026
aure
Uwargida Sarautar Mata

Kuskure Goma (10) Da Matan Aure Ke Yi A Gidan Miji

May 16, 2026
Next Post
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

June 21, 2026
An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 21, 2026
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

June 21, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

June 21, 2026
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

June 21, 2026
Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026
Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada

Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada

June 21, 2026
Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

June 21, 2026
Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni

Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni

June 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.