Abu Uku A Kan Mutun Uku Ababen Lura

Lura

Daga Mahmud Sabo Wushishi,

 1. Abu uku dole ga malami ko mai wa’azi ko mai nasiha ya rika tunasu cewa yana tare da su, domin kada ya dauki kansa ya ajiye inda ba gurbinsa ba,  a matsayinsa na kasasshe; domin shi ba ma’asumi bane da Allah ya katange su a kan sa, ga su guda uku.
 2. Abu na farko mai karancin ilimi ne shi kowanene, karancin iliminsa akan magabatansa ko nata, yafi nisa, nisa ko kusa ba, da wanda yake ko take ilimantarwa, ko yi ma wa’azi ko nasiha don gudun shiga uku.
 3. Abu na biyu karancin binciken littafan mallamai na fannin wannan ilimi da yake bayarwa ko take bayarwa, domin littafan wannan fanni ko saninsu da adadinsu ba’a yi ba, bale abin da ke cikinsu, dan kadan ne sanin mu akan komi. Sai na uku.
 4. Abu na uku karancin shekaru, komi shekarunka ko shekarunki ya yiwu akwai nagaba kuma cikin irin wannan ilimi, wanda hankalin masani akan fanni karuwa yake yi ba raguwa ba, sukenan uku, karancin ilimi da bincike da shekaru, mutun nakan wadannan abubawa guda uku.

AGOGO MAI KYAWO YANA TAFIYA NE DAIDAI DA ‘YAN’UWANSA NA KUSA DA NA NESA:

 1. Agogo mai kyawo, mata da miji, diya da iyaye, kanni da yanni, ana ganinsu tare ne kamar ba su sabani, in kuma suna yi sunanan dai hade, haka ake ganinsu tare suna kusa ko suna nesa.
 2. Agogo mai kyawo, sakan da motsa dogon hannunsa da na minti matsakaici da na awa gajere, in dai suna lafiya suna tafiya da lokaci daidai ne wadaida a cikin duniya a kusa suke ko suna nesa.
 3. Agogo mai rikici da wanda ya lalace duka halinsu daya kamar mutani ne, gyaransa ya koma yanda ake so, abu ne mai wuya, sai sa’ar gaske, ba su daidaituwa da na nesa ko na kusa.
 4. Agogo ko nawanene mai daraja da tsada ko holoko mai araha, ba’a shiga tsakaninsu, sakan ko minti ko awa, ko kuma da ‘yan’uwansa ko kai wanene, haka yake ga mutumi mafi kusa.
 5. Agogon kura mai araha wanda ba ya aiki irin wanda ake saye ma yara, to daidai suke da yaran, babu ruwansu da na kusa dake tare da su bale na nisa, sai dai mai son sa.
 6. Agogon kura da ya lalace da bai lalace ba duk daya suke da yara masu shi, ba su sanin sun lalace ko susan wanda ya lalace a cikinsu a’a kowa daidai ne mai kyawo da mara kyawo na nesa ne ko na kusa.
 7. Agogon mutum ya kan kasance kamar mai shi, in yaro ne in babba, in ba ya hankali ba ya tafiya daidai, sai ya rika latti ko gudu, tsaiko ko garaje, a cikin irin tafiyarsa.
 8. Agogo kamar mutum ne in ba ya da hankali, sai ya yi kara ko ya motsa ba inda ya kamata ba, ya tsaya ba inda ya kamata ya tsaya ba, ko ya wuce inda ya kamata ya tsaya shi ba ruwansa.

DA NAKWARAI WAJEN UBA SHINA; KUMA SIRRIN UBA NE:

 1. Da nakwarai a wajen ubansa shina, kuma shi sirrin ubansa ne, ba ni ba ki abina kuma ina cin naki da wani, ko ke ki ba ni abinki in ci da wani da sirrin uba ne.
 2. Da nakwarai a wajen ubansa ke wanyewa da iyaye lafiya, kuma shine Allah ke hadawa da ‘ya’yan kwaran kokuma shi a ko’inane.
 3. Da nakwarai ko da na shedan ne, inda yana da mata, ko da na fir’auna da karuna da hamana da namaruzu, uwa ta kasan matar Nuhu, in dan nakwarai ne zai kyautata wa uban sa ne.
 4. Da nakwarai ba ya bin ta kanin uba ko yanni uba, bale ta kaninsa ko yanninsa ko wani can daban, yana saba ma iyayensa biyu uwarsa ko uba saboda sai in wawa ne.
 5. Da nakwarai Allah ne yake bi, Anni Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; da ubansa ko uwarsa na raye, ya kabarta sallah suka kira shi za ya yanke ne.
 6. Da nakwarai ba ya son a baci ubansa ko uwarsa, ko da kakansa da magabatan ubansa ko a banzatar da su, bale shi ya bace su ko ya banzatar da su, sai in diyan wawaye ne.
 7. Da nakwarai kowane shi ko iyayensa, sunanan a matsayin iyayensa ne, ko sun fi kowa lalacewa ne, ba’a rama wa iyayen abinda iyaye suka ya masu ko da ganganne kuma koda kashewa ne ta ko’ina ne.

MUTANEN BANZA SUN FI SON DAN BANZA KO A HUKUMANCE:

 1. Mutanen banza ko ga gwamnati sun fi son yayan banza, sune suke gabatarwa, wai sune basu da iyaye ko ba’a san iyayensu ba, shegu ne ko iyayen sun bace.
 2. Mutanin kirki ke kokarin gyaran na kirki da na banza domin duka nasu ne, amma mutanin banza na banza nasu, da sune suke koshi ko a hakumce.
 3. Mutanin banza bai sanin na kirki a hakika, amma mutanin kirki da na banza a hakika in na banza ya san na kirki ta baci masa ko a hukumce.
 4. Mutanin banza yawa suke takama da shi, su kawa mutanin kirki karfi suke takama da shi, kasaitar mata da ya’ya’ da gida da abin hawa da sutura na mallakinsa ne ko a
 5. Mutum na yin daraja ne a idon mutumin kirki an fi kin sa, saida masu sonsa ne ke da karfi koda a
 6. Mutumin da ya gina abin kirki ko abin banza yana da kima ga idanun irin nasa koda zai canja hali, kasar da aka yi gini da ita, ta fi abinda aka gina ko a hukumce.
 7. Mutumin da ya yi gini mai kyawo ko mara kyawo, komi girma da darajar zaure ko kaskanci, kasar da aka yi ginin da ita ta fi ta, bale wanda shine ya gina su ko a hukumce.

ALLAH MAI HALITTA KOWANI IRI DA IRI AKASINSA:

 1. Allah mai halitta kowane iri da irin akasinsa, in kai mai raunin halitta ne a wurin wani ko wata sai ka yi karfi, a wurin wani ko wata kuma akasinsa.
 2. Allah mai halitta, wasu na gabatar da amarya ce kafin akai mata kayanta, wata ta kan dade ba’a kai mata kayanta ba, wata kayan suke gabatarwa akasinsa.
 3. Allah mai halitta da akasinsa, wasu tarbiyar da suke koya ma ‘ya’yansu girman kai ko girmama kansu kamar wasu ‘ya’yan sarauta, wasunsu kawa akasinsa.
 4. Allah mai halitta, tarbiyyan mawadata nuna ma nasu wadata, wasunsu akasin haka, tawali’u da tattali wasu kan nuna ma nasu, ba don rashi ba, sun san wuyan akasinsa.
 5. Allah mai halitta, ga masu mulki ga masu wadata ga masu ilimi, an zo duniya da akasinsu, ba mai mulki ko dan sarki, ba mai dukiya ko dan mai wadata ko mai ilimi sai dai akasinsa.
 6. Allah mai halitta, yana azamu akan masu sauki muna aza kan mu akan masu tsanani da nufinsa, don mu hakura ko mu yi kwadayi ta hanyarsa ko ta hanyar akasinsa.
 7. Allah mai halitta da ikonsa da ba da zabin ga bayinsa, wasu na binsa da tawali’u, wasu ba su binsa suna ja’inja da umurnin Allah a kan mu, wasu kawa ba ruwansu da dayan su, ba Allah ba Manzon Allah ba shedani da yake akasinsa.

AKAI AMARYA KAFIN AKAI MATA KAYANTA:

 1. Akai amarya dakinta kafin akai mata kayanta, a ketarar da mutum hayi ko a kai shi sansani kafin akai masa kaya ko akai mata, ango ya zo ya taras da amarya da kayanta.
 2. Akai mai kaya matsera kafin akai kayansa, in ba mai kaya yana amintaccen wuri mai kama da gidansa, kamar wanda ke wajen aikin Hajji ko hukuma amintatta.
 3. Akai amarya dakinka, ko da tana dauke da kwarkwata, da kwai da kwarkwata duka mallakan gashi ne, na mai kazanta ko tufafinsa ko nata, ya fi ace an aske gashinta.
 4. Akai matalauci wurin sana’a ko wurin aiki ko kasuwa, wanda ransa ya baci ko ya yi fushi ko wata hasara hakuri ake ba shi ko gudummawa, in jahilci ne ace ya je makaranta.
 5. Akai mara lafiya wurin magani, kuma a rika zuwa ana gaishe shi ko gaishe ta, da taimakawa in da bukatar haka, in hauka ce akai masa dauki zuwa turu a gidan mahaukata.
 6. Akai mai mugun hali ga hukuma ko wurin masu yin wa’azi da tarbiya, mara lafiya ne kadai ake son zuwa a gaishe shi, domin shine ke cikin damuwar mafi kusanta.
 7. Akai wa mara lafiya dauki da sauri shine ya fi duk wani mai damuwa kusanci da abin da ke damunshi ko ita, gabobin jiki ne, ba kamar wanda za ka bari bane ka kaurace cikin makusanta.
 8. Akai wa masu fada dauki a raba su a ba su hakuri, ba kamar mara lafiya bane mai bukatar gaisuwa ko tallafi na abinci da magani ko tallaba, da jiki ya motsa fada da wani zai tsaya, bale talauci da ke nisa da sannu yake kusanta.

BA’A WASA DA ABINDA BA NA WASA BA:

 1. Ba’a wasa da abin da ba na wasa ba, ba’a wasa da addini, ba’a wasa da rai da lafiya, ko rashin lafiya ko zama lafiya, da abinda zai shafi magabata tun ba makusanta ba.
 2. Ba’a rasa komi a kasuwa na banza da na kirki, ga abin sayarwa da masu sayarwa, a hannun na kirki ko na banza a kasuwa, “inda adalci dambu bai rasa mai ko bai ji mai ba?
 3. Ba’a rasa mai a dambu inda adalci komi yawansa, sai dai ko in an rena dambun, kokuma man da aka sa masa, domin ba’a dambu babu mai, in ba inda ya zama tilas ba.
 4. Ba’a wasa da kaifi ko wuta ko maciji ko kunama, in ba an shirya wata ‘yar dabara ba, ko an dogara sosai da Allah ba da yi masa ganganci ba, bari susa inda bai maka kaikayi ba.
 5. Ba’a son susa ga miki ko ga kurji balantana akan gyambo wasa da macuci ko wanda ya fi karfinka mutum ne ko ba mutum ba, domin ba’a wasa da abin da ba na wasa ba.
 6. Ba’a wasa da sallah kuma barinta komi dadi komi wuya, domin sakamakon yin ta ya fi komi dadi, na kin yin ta kuma ya fi komi zafi da wahala, ba don rashin sani ba.
 7. Ba’a wasa da abin da ba na wasa ba, don a ji dadi a yi dariya ko a sami kudi, abin da mutanin duniya ke so ba shine na masu lahira ba, ba kuma shine suke so ba.
 8. Ba’a wasa da duniya bale a yi da lahira, ba’a wasa da mutum da aljani da shaidani bale a yi wasa da Allah da Manzonsa da Kur’ani ko Hadisi da mallamin kirki, sai in mutum ba mai hankali ne ba.

Wushishi ya rubuto daga Bosso, Jihar Neja

08055736329, 08034358678

Exit mobile version