Ko shakka babu cutar gyambon ciki wato Ulcer wata cuta ce wadda ke damuwar kusan kowa, hakanan cutar tafi damuwar mata fiye da maza wannan kuwa ya kasance hakan ne sakamakon sakakin su da yawanyin amafni da yaji.
Bugu da kari kuma cutar takan takura ma lafiya, matuka.sannan ita wannan cutar bactria wato kwayar cuta ma na haddasa ta wadda ake kira da suna Helicobacter Pylori.saboda kasancewar ita wajen zamanta a cikin ciki ne.bayannan kuma akwai wani sinadari mai taimakawa wajen narka abinci mai suna (pepsin) wanda gastric gland ke fitarwa shi ma yakan haddasa gyambon ciki, tare da wasu acid din na cikin ciki..Akwai kuma shan magunguna barkatai,to dukkan wadannan abubuwa su kan jawo cikin mutum ne yai rauni ko kujewa. Ko dai a wajen karamin hanji wato Duedonum ulcer) ko a saman ciki wato (peptic ulcer) ko wajen kirji wato (Epigastric ulcer) Daga nan se alamun ulcer suke baiyana duk lokacin da aka bukaci abinci babu, ko ka sha yaji ko tsami ko abu me gas.
Alamomin Ulcer sun hada da
Idan kuma ta zama babba manyan hanyoyin kamuwa da Ulcer kuma sun hada da;
yawan shan magani barkatai ba akan kaida ba masu illa ga fata misali; pracetamol,iburopen da kuma Aspirin.
Har ila yau kuma ita kwayar cutar nan Helicobacter Pylori ita ma tana haddasawa.
.Acid din dake cikin mutum shima yana haddasawa
sannan yawan cin yaji me zafi shima yakan haddasa ta
.sai kuma pepsin wato sinadarin dake da alaka da shiga da narkewar abinci a cikin ciki.Saboda haka ne duk lokacin da ba,a ci abinci ba a cikin ciki, shi wannan pepsin din ya kan fitar da wani ruwa me dafi dake narka abinci. To idan ya tsarto da ruwan bai samu abincin da zai narka ba sai kuma ya yi ma ciki rauni, shi ake kira ulcer. Da zarar kaci abinci wanda ke da yaji, tsami, gas ko zafi sai wurin da yai raunin yayi ta maka ciwo,.ko kuma da ka dade baka ci abinci ba, sai wurin ya rika ciwo. Amman ga marar ulcer yunwa bata kawo ta.
Abubuwan da ake so mai fama da ulcer ya kiyaye
- Ya daina shan wan abu kamar tsamiya, lemun tsami fura mai tsami da dai sauransu
- Wani abu mai yaji kamar su yaji,
- Abu mai gas irinsu lemun kwalba. Amma zaka iya shan maltina.
4, Abunci mai zafi kar aci har sai ya huce dan gudun kada asamu matsala a raunin
5 Shan magani ba akan ka’ida ba da kuma cin abinci ko wanne lokaci.