Abubuwan Da Suka Fi Dacewa Mace Ta Yi A Bikin Sallah –Amira Rakiya

Ana wa Sallah kirari da “mai biki daya rana” ko kuma a ce “ta wuce ta bar wawa da bashi”. Duk wannan hannunka-maisanda ne ake wa mutane kar su dauki lamarin bukukuwan Sallah da zafi. Maza a bangarensu abin yakan zo da sauki saboda dangana da abin da ya zo hannu a yi amfani da shi, amma a bangaren mata ne ake samun ‘yar hatsaniya wani lokaci inda wasu ke tayar da hankulan mazajensu kan ala dole sai sun yi musu abin da suke so ko-ana-ha-maza-ha-mata. Wannan dalili yakan hargiza gida, idan ma ba a yi sa’a ba sai ya zama sanadin yin Sallah cikin kunci a cikin iyali. Domin rigakafin wannan, Editanmu Abdulrazak Yahuza Jere ya taba zantawa da wata Malamar Addinin Musulunci don bayyana wa mata hanyar da ta fi dacewa su yi shirin sallah. Ga tattaunawar tasu:

 

 

Da wa muke tare….

Wa alaikumus Salam. Kana magana da Mrs Rakiya Shehu Bamalli. Ameerah ta Jamaatud Dawah Fouad Lababidi Islamic Academy da ke Wuse Abuja.

 

Sallar Idil Fidir ta zo, a matsayin mace ta mai shirya iyali domin bikin sallah, wadanne matakai ne kike ganin ya dace mace ta bi domin tabbatar da cewa iyali sun yi sallah cikin nishadi?

Alhamdulillah, akwai abubuwa da dama da Mace ya kama ta ta shirya domin bikin Sallah. Misali, yin hakuri da abin da ta samu wajen maigida musamma sanin halin da kasa me ciki, kar ta yi dogon buri Na cewar dole sai tayi sabon dinki, idan ta san maigida ba shi da halin yi ta yi hakuri da abin da take da shi domin zanin sallah ba dole ba ne a musulunci. Yin hakuri da tattali wajen yin abincin sallah, shi ma a duba yana yi idan da hali a dafa da dama har a raba wa makwabta, idan babu a dafa wanda ya samu ba tare da tashin hankali ba, domain yin abinci a raba ba dole ba ne. Bugu da kari uwargida ta yi hakuri da duk abin da maigida ya bata, idan tana da halin yin kari ta yi.

 

A ganinki mene ne hakkokin da ya kamata maigida ya sauke na shirye-shiryen bikin sallah?

Hakkokin da maigida ya kamata ya sauke lokacin bikin sallah sun hada da: farantawa iyali rai ta hanyar samun canjin abinci da abin sha da sutura idan yana da hali idan ba shi kuma a basu magana mai dadi. Maigida kuma ya tabbatar yaja iyalinsa zuwa masallacin Idi domin samun ladar da ke cikin wannan rana.tare da su.

 

Ko akwai wasu shawarwari da za ki baiwa uwargida kan faranta wa maigida rai lokacin bikin sallah?

Ina mai ba wa mata ‘yan’uwana shawarar da su yi hakuri da dukkan yanayi da maigida zai kasance a wanna lokaci na bikin sallah, watau abin da ya bayar da shi za a yi amfani kar a matsa.

 

Ziyarar ‘yan’uwa na daga cikin muhimman hidindimun bikin sallah, ko akwai shirin da ya dace mace ta yi na tarbar baki?

Ziyarar ‘yan’wa da abokan arziki abu ne mai mahimmanci a lokacin bukukuwan sallah, don haka iyaye su yi shiri da kyakkyawan tsari na musamma domin ganin sun shirya karbar baki da kuma tura yara zuwa ziyarar ‘yan’uwa da abokan arziki. A wannan lokaci uwargida na iya tanadin abin da ya saukaka a gare ta domin maraba da baki kamar cincin, minti, goro, nama ko ma ruwa ne kawai wato daidai karfin aljihu.

 

Wasu yara musamman matasa na amfani da lokacin bikin sallah wajen aikata ayyukan assha a matsayin murnar sallah, me ya kamata iyaye su yi don rigakafin wannan?

Lallai ana samun bata-gari a lokuttan bikin sallah, a nan ina mai ba iyaye shawara da su ja kunnen ‘ya’yansu a kan irin abubuwan da ba su da kyau da kuma yi masu nasiha da kar su yarda su aikata. Tun kafin ranar sallah ta zo ya dace iyaye su yi wa ‘ya’yansu nasihar tare da nuna masu illar yin hakan.Insha Allahu idan suka yi musu hakan za a samu nasara.

 

Wasu bata-gari kan yi amfani da lokacin bikin sallah wurin aikata ha’inci a gidajen mutane, me ya kamata matar ta yi wajen sanya ido da rigakafin aukuwar hakan?

Duk da yake hidindimun gida suna da yawa a kan mace, amma ta yi kokarin sanya ido sosai ga mutanen da ke kai komo a cikin gidanta. Wasu suna zuwa ne ba don Allah ba sai don neman yin abubuwan da ba su dace ba kamar dauke-dauke da sauransu. Don haka mace kar ta shagala har ya kai ga ta kasa tantance masu shigo ma ta gida. Mutumin da yake da gaskiya ba boyayye ba ne, haka nan maha’inci ma za ka yanayinsa a bayyane. Idan ya shigo gida zai rasa takamaimen inda zai nufa, zai rika kale-kalle na babu gaira babu dalili, zai nemi hanyar da za a yi a bar shi a wani wuri ya zauna shi kadai ko ya kirkiri wata sabga da zai yi a cikin gidan mara amfani. Duk wannan ya dace mata su sa ido a kai sosai. Sannan a kara da addu’a.

 

Ko akwai nasihar da ya kamata mace ta yi wa ‘ya’yanta kafin su fita zuwa gaishe-gaishen sallah?

Nisihar da zan yi ita ce , kira ga iyaye maza da mata da mu ji tsoron Allah, mazaje idan muna da hali mu kyautata wa iyalinmu a wannan lokaci mai albarka, sannan mu mata mu san yanayin da mazajenmu ke ciki. Mu yi hakuri kar mu takura masu, sanan mu ja ‘ya’yanmu a jiki tare da yi masu nasiha da basu shawarwarin da suka dace, da kuma yi masu addu’ar fatan shiriya. Allah ya sa mu yi hidimar sallah lafiya ya bamu ladar ibadun da muka yi; ya maimaita mana amin summa amin. Mun gode

 

Exit mobile version