Achraf Hakimi ba ɗan wasan baya ba ne kaɗai, fitaccen ɗan wasan Afrika ne wanda tauraronsa ya haska a duniya. A makon da ya gabata ne, ya lashe Gwarzon Ɗan Ƙwallon Afrika na 2025, wanda ya zama ɗan baya na farko cikin shekaru 52 da ya samu wannan lambar yabo.
Tarihin Rayuwarsa
An haifi Hakimi a Birnin Madrid na ƙasar Sifaniya a shekarar 1998, asalin iyayensa ‘yan ƙasar Maroko ne. Ya taso a unguwar talakawa da ke Getafe. Tun farkon ƙuruciyarsa yaro ne mai son taka leda, kuma bai daɗe ba ƙwarewarsa ta kai shi ƙungiyar matasa ta Real Madrid. A nan ne ya fara samun horo da gogewa.
- Dalilin Da Ya Sa Muka Tafi Amurka Don Taron Tsaro – Gwamna Radda
- Gwamnatin Tarayya Ta Umarci A Fara Karatun Digiri Da Yaren Tibi Da Nupe A Jami’o’i
Tauraronsa Ya Haska A Turai
Hakimi ya yi fice sosai lokacin da Real Madrid ta kai shi aro zuwa Borussia Dortmund. A nan ne ya nuna kalar ƙwarewarsa wajen murza leda: tare ƙwallo a matsayin ɗan wasa baya tare da kai-hari, gudu, da iya sarrafa kwallo.
Daga Dortmund ya koma Inter Milan, inda ya samu sabbin dabarun sarrafa ƙwallo a fili, ya kuma taimaka wa ƙungiyar wajen samun manyan nasarori. Daga bisani ya koma Paris Saint-Germain (PSG), inda ya tauraronsa ya ƙara haskakawa sosai.
A PSG, Hakimi bai tsaya taka ƙwalla a matsayin ɗan baya ba kaɗai, yana taimakawa wajen zura ƙwallaye a ragar abokan hamayya, yana kai farmaki, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙungiyar.
Ɗaga Martabar Tawagar ‘Yan Wasan Maroko
Hakimi na taka leda ne a tawagar ‘yan wasan Maroko, kuma wannan shi ne abin da ya fi alfahari da shi. A Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022, ya taka muhimmiyar rawa da ta kai Maroko zuwa matakin kusa da na ƙarshe, wanda babban abun alfahari ne ga ƙasar da kuma Afrika.
Hakimi kuma mutum ne mai matuƙar son kasancewa iyayensa. Bayan buga wasanni, ya kan tafi ya rungumi mahaifiyarsa a filin wasa, wanda hakan ya a taɓa zuciyar masoyansa sosai.
Shekarar Da Ya Kafa Tarihi A PSG
A 2025, Hakimi ya taka wasa mai ban mamaki tare da PSG. Ya lashe gasar zakarun Turai ta Champions League, Ligue 1, Coupe de France, da UEFA Super Cup. Wannan gagarumar nasara ta sa ya doke fitattun ‘yan wasa kamar Mohamed Salah da Victor Osimhen, wajen lashe Gwarzon Ɗan Ƙwallon Afrika na 2025.
A jawabin karɓar kyautarsa, ya ce wannan lambar yabo “ba tawa ba ce ni kaɗai, ta dukkanin matasa maza da mata masu mafarkin zama ‘yan wasa a Afrika ce.”
Halayyarsa A Wajen Filin Wasa
A zahiri, Hakimi mutum ne mai nutsuwa da ladabi. Abokan wasansa suna yaba masa kan yadda halinsa da aiki tuƙuru yake. Ba ya son hayaniya ko jita-jita, aikinsa a fili shi ne yake bayyana wanw irin mutum ne.
Burin Da Ya Cimma
Zama Gwarzon Ɗan Ƙwallon Afrika a matsayin ɗan baya babban tarihi ne. Ya nuna irin ci gaban da Hakimi ya yi fatan samu a harkar ƙwallon ƙafa. Ya nuna cewa ko a ɓangaren ‘yan wasan baya, akwai gurbin taurari kamarsa.
Yanzu Hakimi yana da shekaru 27 kacal a duniya, amma ya kafa tarihin da zai daɗe ana tunawa da shi. Ɗan wasa ne da ke tsakanin Turai da Afrika, wanda ke nuna ƙwarewarsa a kowace nahiya ya tsinci kansa. Kuma babu shakka, labarinsa ya nuna yadda jajircewa da himma suka kai shi ga zama tauraro.














