DAGA SADIK TUKUR GWARZO
Cigaba daga makon jiya
Bayan kura ta lafa, sai Gwamna Luggard ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da ya ke turawa lokaci zuwa lokaci gami da labarta mu su abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shi ne har ya ke fada mu su cewa, ba lallai ne a ce tafintan Kyaftin Moloney da gayya ya yi wannan kasassabar ba, sai dai watakila hakan ta faru ne, saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney ya yi dangane da yaren Hausa ta yadda har ya kasa tantance tsakanin abinda ya ke karantawa da abinda tafintansa ya ke fada.
Don haka a karshe Luggard ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari a nan gaba shi ne Turawan mulki ’yan uwansa su koyi Hausa. Wannan ya na cikin D.J.M Muffet, concerning Brabe Captain, London 1964.
Ai kuwa hakan a ka yi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami’inta ya fara koyon harshen Hausa. An buga sanarwar fara yiwa jami’an mulkin mallaka jarrabawar auna fahimtar harshen Hausa a jaridar Northern Gazette ta ranar 30 ga watan satumbar shekarar 1902.
Rubutun Boko Na Farko
Sai dai abu ne mai matukar wuya a gane wanda ya fara rubuta Hausa da haruffan Romawa (Rubutun Boko) kasancewar bauta da kasuwanci sun sanya Hausawa shiga kasashen Larabawa lokaci mai tsawo da ya gabata. Daga can kuma an tsallaka da wasu izuwa yankunan Turai da sauran sassan duniya masu nisan gaske duk da zummar yin bauta.
Kowa ya san an yi zamunna na cinikin bayi a baya, sannan shaharar masautar Borno ba karamar aba ba ce. Ita ce a ka ce sarakunanta sun shahara har ma a ka ce a wajajen karni na 11 su ka fara hurda da Larabawa, sannan kuma idan yakinsu ya motsa, mamaya su ke kawowa dukkanin makwabtan kasashe, ciki kuwa harda kasar Hausa.
An ce, tun zamani mai tsawo da su ka gabata akwai Hausawa masu yin bauta a Turabulus da makwabtan kasashe, wadanda a ke kyautata zaton daga Borno a ka kwashe su izuwa can.
Ta na iya kasancewa wani daga Turawa ko Girkawa ya taba jarraba amsar labaru daga wani Bahaushe gami da rubuta shi da Romanci (Boko), amma abin bai fito ga duniya har mun riske shi ba. Amma dai mafi dadewar rubutun Boko da a ka samu shi ne wanda Marubuci Ibrahim Yaro Yahaya (Allah Ya ji kansa da rahama) ya kawo a shafi na 74 na littafinsa mai suna ‘Hausa A Rubuce.’ inda ya ke cewa, “Watakila za a yi mamaki a ji cewa a kasar Denmark ta Turai a ka fara samun an rubuta kalmomin Hausa a cikin rubutun Boko tun a karni na 18.
Yadda abin ya faru shi ne a cikin shekarar 1772 sarkin Denmark ya tura wakilansa izuwa Arabiya, don gudanar da bincike na kimiyya. A cikin wakilan har da wani mai suna B.G Neibuhr, wanda shi ne kadai ya tsira kuma har ya koma gida kasarsa.
To, a wannan shekarar sai wani Balaraben Tunis ya je Denmark ziyara. Sunansa Abdurrahman. A tare da shi akwai wani bawansa Bahaushe. Sai sarkin Denmark ya sa a ka kira Niebuhr, domin ya zama tafinta tsakaninsa da Balaraben nan, kasancewar shi Niebuhr ya koyi Larabci a tafiyar da yayi izuwa Arebiya.
To, a wannan gamin ne har abota ta kullu tsakanin Niebuhr da Abdurrahman, har kuma Niebuhr ya yi sha’awar koyon Barbarci da Hausa daga wannan Bawa. A nan ya dukufa ya na koyo, a na fada ma sa kalmomi ya na rubutawa da Boko.
Ga wasu kalmomi da a ka samu Niebuhr ya rubuta a Hausar Boko, kamar yadda ya ji daga bakin wannan bawa Bahaushe.
Dudsji – Dutse
Ghaui – Gari
Dsjenari – Zinari
Ghurasa – Gurasa
Crua – Ruwa
Sirki – Sarki
Schensali – Shaidani
Berni – Birni
Na baya daga wannan kuma shi ne rubuce-rubucen da Baturen Mishan mai suna J.F Schon ya yi da Hausa a wuraren 1856 lokacin da ya roki Dr. Barth ya ba shi aron yaransa biyu, Dorugu da Abega, don su taimaka ma sa wajen yin rubututtukan Hausa.
A wancan lokacin ne Dorugu ya rika fadar labarun Hausa, shi kuma ya na rubutawa, har a ka samu cewa J. F Schon din ya rubuta litttattafai. Misalin magana Hausa, Littafin Musa na fari, Labari Nagari, Dictionary of the Hausa da sauransu.
Bunkasar Rubutun Boko
Amma dai idan mu ka dawo maganar asalin soma rubuta Hausa da Boko irin wadda har yau mu ke amfani da ita, to zai fi kyau mu koma kan maganarmu ta sama cewa Turawan mulkin mallaka ne su ka assasa tare da tabbatar ma na da ita.
Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar ma na da hakan a shafi na 55 na littafinsa mai suna ‘The Hausa factor In West African History’. Kuma ga kadan daga abinda ya ce:- Karatu da rubutu ta hanyar Boko ya samu ga Hausawa ne a farkon karni na 20.
Saboda a shekarar 1900 AD ne gwamnatin Ingila ta karbe ragamar mulki daga hannun sarakunan Hausawa, amma sai a 1903 sojojin Gwamna Luggard su ka cinye Kano da Sakkwato a yaki, sannan su ka bude makaranta ta farko a Sokoto tare da malamai biyu, watau Mr. Kurdan da mataimakinsa Malam Ibrahim, amma makarantar ba ta dade ba, saboda iyaye sun ki sanya ‘ya’yansu, don gudun kada a cusa mu su akidar Kiristanci.
Farfesa ya nuna cewa rashin gamsuwar Hausawa ga ilimin da Turawa su ke shirin ba su dadadden abu ne, kuma tun a wancan zamanin kalmar ‘Boko’ ta samo asali wadda a cewarsa ma’anar ta da Hausa shi ne kamar a ce ‘rufe kura da fatar akuya’ (watau a yi basaja wajen rufe wani abu da wani abu).
Tun kafin wannan ma, shi kanshi Luggard sai da ya kalli Hausawa da yadda su ka yi riko da addini tun a lokacin, sannan ya yi amannar cewa bai yiwuwa a ce za a koyar da su Boko kamar yadda a ke koyar da shi a kasarsu Ingila.
A wani zancen kuma, cewa a ka yi tun sa’ar da Luggard ya ke yaki a kasar nan ya fara sanyawa a na rubuta Hausa ta hanyar amfani da rubutun Romawa (Boko). Saboda kamar yadda mu ka fada tun a baya Lugga ya fahimci tasiri da bunkasar yaren Hausa a wannan yanki na Arewa, amma kuma a wurinsa bai yiwuwa ya rubuta Hausa da ajami kamar yadda ya samu Hausawan lokacin su na yi.
Dalilan yin hakan su na da yawa. Daga ciki akwai fadin cewa idan za a rubuta Hausa da ajami, sai an koyi yare biyu maimakon daya, watau sai an koyi Hausa, sannan kuma an koyi Larabci. Amma watakila babban dalilin ya fi ga kiyayyarsu ga Larabawa ko kuma a ce kiyayyarsu ga Musulunci (kamar yadda babban dalilin kin jinin Boko daga Hausawa shi ne kiyayyarsu da Kiristanci tunda watakila da a ce Musulmai ne su ka kawo ilimin zamani kasar Hausa da ba za a yi artabu da iyaye wajen su sanya ‘ya’yansu ba).
Akwai wani abu ma da ba sai an boye ba. Luggard ya fada cewa ba ya ganin rashin sanya Musulmai a cikin sojojinsa a matsayin siyasa, amma a zahiri siyasar ne. Tunda dai kusan daukacin sojojin nasa ba Musulmai ba ne, mutane ne Gwarawa da sauran kabilu marasa addini wadanda su ke adawa da Musulunci, wadanda kuma yawa-yawansu su na da matsala da Musulmai tun a lokacin jihadi. Don haka su na zuci-zucin karya daulolin da Musulmai su ka kafa, domin daukar fansa.
A daya ɓangaren kuma, akwai kwatankwacin wannan kiyayyar a zukatan Hausawa, kuma ta na daga manyan dalilan da ya sa Hausawa su ka kyamaci ilimin Boko. Tunda ilimin ya zo ne daga wadanda su ke gani a matsayin makiyansu. Shi ya sa sai da a ka sha-burtu a ka soma sanya yara a makarantun zamani a wancan lokacin, koda yake har izuwa yanzu (kusan shekaru 114 kenan) wasu daga cikinmu Hausawa na kallon ilimin Boko a matsayin haramtaccen abu kuma gurbatacce.