ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, October 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

by Abubakar Sulaiman
51 minutes ago

An kwashe mara lafiyar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola daga Nijeriya zuwa ƙasar Switzerland domin ci gaba da kula da lafiyarta. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a na Nijeriya, Muhammad Ali Pate, ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Matar mai shekaru 42, wadda aka tabbatar tana ɗauke da nau’in cutar Ebola mai suna Bundibugyo, ta tashi daga Abuja da jirgin ɗaukar marasa lafiya na musamman. Pate ya ce lafiyarta ta inganta sosai, tana cikin hayyacinta, tana iya magana, kuma sakamakon gwaje-gwajen lafiyarta na komawa kusa da yadda ya kamata (warkewa).

An kuma haɗa da mijinta zuwa Switzerland. Ministan ya bayyana cewa mijin nata, wanda ɗan diflomasiyyar Switzerland ne da ke aiki a Abuja, bai nuna alamun kamuwa da cutar ba. Sai dai ya jaddada cewa ingantuwar lafiyar matar ba na nufin ta daina yaɗa cutar ba, saboda haka aka bi ƙa’idojin kariya masu tsauri kafin a kwashe su.

ADVERTISEMENT

Bayan tabbatar da kamuwa da cutar a ranar 20 ga Oktoba, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce an gano mutane 53 da suka yi hulɗa da mara lafiyar, ciki har da ma’aikatan lafiya, da ma’aikatan gida da mijinta. An sanya su cikin tsarin sa ido domin gano duk wata alamar kamuwa da cutar.

Matar ta dawo Nijeriya daga Uganda ta hanyar Addis Ababa a ranar 3 ga Oktoba, sannan ta fara nuna alamun rashin lafiya bayan kwana huɗu. Hukumomin lafiya na ci gaba da bincike domin gano yadda ta kamu da cutar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

Ministan ya buƙaci ƴan Nijeriya su kasance cikin shiri, su bi bayanan da hukumomin lafiya masu sahihanci ke fitarwa, tare da haɗin kai da jami’an kiwon lafiya.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Adadin Waɗanda Aka Kashe A Harin Ƴan Bindiga Ya Kai 50 A Taraba
  • Abubakar Sulaiman
    Kano Da Wasu Jahohi 7 Da Ake Hasashen Samun Hazo Yau Litinin – NiMet
  • Abubakar Sulaiman
    NDC Ta Caccaki Tinubu Da APC Kan Raba Motocin Prado Na Sama Da Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Pantami, Gwarzo, Da Adebutu Ranar 29 Ga Oktoba

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola
Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Hukumomi Su Ƙarfafa Wayar Da Kai Kan Cutar Ebola

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi  A Katsina
Kiwon Lafiya

Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aikin Gargaɗi A Katsina

October 19, 2026
Likitocin Ƙwaƙwalwa 250 Ne Kacal A Nijeriya, Ragowar Sun Gudu Ƙasashen Waje
Kiwon Lafiya

Likitocin Ƙwaƙwalwa 250 Ne Kacal A Nijeriya, Ragowar Sun Gudu Ƙasashen Waje

October 10, 2026

LABARAI MASU NASABA

An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

An Fitar Da Matar Da Ta Kamu Da Ebola Daga Nijeriya Zuwa Switzerland

October 26, 2026
Adadin Waɗanda Aka Kashe A Harin Ƴan Bindiga Ya Kai 50  A Taraba

Adadin Waɗanda Aka Kashe A Harin Ƴan Bindiga Ya Kai 50 A Taraba

October 26, 2026
Kano Da Wasu Jahohi 7 Da Ake Hasashen Samun Hazo Yau Litinin – NiMet

Kano Da Wasu Jahohi 7 Da Ake Hasashen Samun Hazo Yau Litinin – NiMet

October 26, 2026
NDC Ta Caccaki Tinubu Da APC Kan Raba Motocin Prado Na Sama Da Biliyan Ɗaya

NDC Ta Caccaki Tinubu Da APC Kan Raba Motocin Prado Na Sama Da Biliyan Ɗaya

October 26, 2026
Akwai Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa Masu Rajista Fiye Da 500 A Kano – Ahlan

Akwai Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa Masu Rajista Fiye Da 500 A Kano – Ahlan

October 26, 2026
INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Pantami, Gwarzo, Da Adebutu Ranar 29 Ga Oktoba

INEC Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Pantami, Gwarzo, Da Adebutu Ranar 29 Ga Oktoba

October 26, 2026
Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.