Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Enduring Peace ta yi ƙarin haske kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna taƙaddamar sojoji da jami’an ƴansanda a ƙaramar hukumar Bassa da ke jihar Filato. Rundunar ta ce sojojin sun je yankin ne bayan samun kiran neman agajin gaggawa kan harbe-harbe da kuma kisan wani mazaunin yankin.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Chinonso Oteh, ya fitar ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, rundunar ta ce a ranar 20 ga Oktoba, dakarun sashi na Uku na Operation Enduring Peace sun samu rahoton harbe-harbe a Mai Farin Moto, Maraban Dere da wasu al’ummomin da ke maƙwabtaka da su a Bassa. Rahoton ya kuma ƙunshi kisan wani mazaunin yankin mai suna Adamu Suleiman.
Rundunar ta ce an tura sojojin domin tantance halin tsaro, da gano abin da ya faru, da hana rikicin yaɗuwa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Bayan isa wurin, sojojin sun yi ƙoƙarin tattaunawa da jami’an ƴansandan da ke yankin domin fahimtar halin da ake ciki da kuma daidaita matakan tsaro.
Sai dai sanarwar ta yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an ƴansandan ba su ba sojojin haɗin kai ba, duk da ƙoƙarin da aka yi na kwantar da hankula da kiyaye ɗa’a. Rundunar ta jaddada cewa matakin da sojojin sauka ɗauka ya samo asali ne daga kiran neman agaji, ba kamar yadda wasu bayanai da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta ke nunawa ba.
Operation Enduring Peace ta ce ana kan tattauna batutuwan da suka taso ta hanyoyin shugabanci da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin gano gaskiyar lamarin da kuma hana sake faruwarsa.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, tana mai cewa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato.














