Connect with us

LABARAI

Adalcin APC Ne Ya Janyo Zaben ‘Yar Tike A Zaben Fidda Gwani -Chika

Published

on

Bukatun kai ne ba na al’umma ba ta janyo canjin sheka musamman ga ‘yan majalisun tarayya, da zababbun shugabannin nan suna tare da jama’a kuma sun yiwa jama’a aiki ba abinda zai sa su canja sheka zuwa wasu jam’iyyun. Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Rafi, Munya da Shiroro, Hon. Abubakar Chika Adamu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a minna kan amincewa da zaben ‘yar tike da jam’iyyar APC ta kasa da ta tarayya ta amince da shi dan fuskantar manyan zabuka masu zuwa.

Dan majalisar ya ce jam’iyyar APC, jam’iyya ce da ta ke tukaho za ta kawo canji, kuma canjin nan ta kawo shi domin a baya dalaget ne ke zaben wanda zai tsaya takara a inuwar ita jam’iyyar, wannan tsarin ‘yar tike tsari ne da aka kawo wanda aka baiwa ‘yan jam’iyya damar tantance wanda za su tura ya jagorance su, ya zama kamar zabe ne na gama gari a cikin jam’iyya. Wannan abin yayi daidai, daman mulki Allah yana ba wanda yake so ne a lokacin da yaso, don haka da ‘yan siyasa za su gane in ka nema ba ka samu ba za ka dauka daga Allah ne ba laifin mutanen nan ne ba su zabe shi ba.

Don haka ina kira ga jama’a indai siyasar suke so na gaskiya kuma ana bukatar raya kasa da jam’iyya ce, to da kar su yarda ayi anfani da su wajen cimma burin wasu, duk wanda ya ce ka tada fitina dan bai ci zabe ba ka sani ba mai sonka ba ne kuma ba mai son ci gaban kasar ba ne na gaskiya. Kowa ya yi kikari kar ya mai da harkar zabe ko rai ko mutuwa, kar ku damu da waye za ku zaba amma ya zama wajibi ku zabi wadanda za su yi maku aiki, duk wanda ke tunanin zai zabi mutum dan ya biya mashi bukata to ka sani ba wani wanda zai iya yi maka komai.

Dangane da maganar kawo karshen siyasar kudi kuwa wannan kuskure ne babba, sau tari mu da ke shugabantan jama’a sai mun bada kudi wajen daukar dawainiyar wasu masu zaben kodai dan nisan wajen zabe ko rashin abin hawa ga masu zaben, sai dai a ce a wannan lokacin an dawo da siyasar ‘yanci da ra’ayi, mai makon a baya ‘yan kalilan ne ke da ikon zabi dan takara wanda kuma yanzu ‘yayan jam’iyya ne keda alhakin kawo dan takarar da zai wakilci al’umma a wajen zabe.

Dangane da canjin sheka kashi cas’in ba suna yi ba ne dan al’umma ba, ba sun yi ba ne dan suna ganin APC ta gaza ba, ai tun farko da aka faro tafiya da sun nuna ba su yarda tafiyar ba, ba su yarda da yadda ake yi ba. Saboda da yawansu ba su yadda za su cimma burinsu ba, sai sun koma can, shi ne suka koma.

Da yawa daga cikin ‘yan majalisar wakilai da na sani sun koma can ne za a basu amincewa ta takara ba hsmayya, hakan ya nuna cewar mutanen nan ba na kwarai ba ne, kai ba gari ba ne. In kuwa kai na gari ne sai ka fadi hujjar da ya sa ka canjin shekar, don haka idan ba jama’a sun dawo akan tafarkin akida ba, sun tun kari siyasar gaskiya ba to lallai irin salon ba inda zai kai kasar nan da siyasar da muke akai ko ina ba sai koma baya.

Don haka ina jawo hankalin jama’a wajen yin zabe na gari da zabar mutanen da ke son ci gaban kasar nan.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: