Addu’a Ce Kadai Za Ta Fitar Da Mu Halin Da Muke Ciki A Kasar Nan

Daga Alhussainn Suleiman

Yakamata al’ummar kasar nan su taimaka wa gwamnati akan kokarin da take yi wajen samar da tsaro domin sai da tsaro da kwanciyar hankali ne harkokin kasuwanci da sauran harkoki za su gudana kamar yadda ake bukata, sannan kuma har ila yau kasashen da ake ganin sun samu cigaba tsaro ne ya kai su ga haka, ya na da kyau mu lura da wannan.Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Hamza Abdulwahab a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin Kano.
Hamza Yellow, ya tabbatar da cewa matukar al’umma suka ba da hadin kai da goyon baya da yardar Allah za a samu shawo kan matsalolin da kasar nan take fama da ita, sannan wani. Sannan wani abu muhimmi da al’umma za su mayar da hankulan akai shi ne a koma ga Allah tare da addu’a dare da rana da nufin Allah ya kawo mana saukin al’amura addu’a. Hamza ya yi amfani da wannan dama da kira ga ‘yan kasuwar kantin kwari da na jihar Kano baki daya cewa su tabbatar sun rike amana tare da sanyan tsoron Allah a cikin harkokin sun a kasuwanci.
Yawancin abin da ya sa ake samun matsaloli a cikin harkokin kasuwanci rashin gaskiya da amana na daya daga cikin abin dake haifar da shi. Alhaji Hamza Abdulwahab, ya taya gwamnan jihar Kano da sarkin Kano da ma daukacin al’ummar musulmin jihar murnar kammala Azumin Ramadan da kuma karamar sallah lafiya , sai ya yi addu’ar Allah ya karawa jihar Kano da kasa baki daya zaman lafiya da kwanciyar hankali.Daga karshe yan godewa al’ummar musulmi musamman masu hali da suka yi amfani da dukiyoyin su wajen ciyar da bayin Allah musamman marayu da marasa galihu acikin watan Azumin Ramadan , da fatan hakan zaim dore ko da bayan watan na Ramadan tan wuce

Exit mobile version