Muazu Hardawa" />

Addu’a Ce Maganin Hasashen Matsalolin Da Za A Iya Shiga A Nijeriya

Ganin yadda harkokin siyasa ke kankama a kasata Nijeriya har an kai ga a na dab da fara gudanar da zaben gama gari, yadda za a zabi shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar mulkin kasa da nufin samun saukin rayuwa da yadda za a magance matsalolin da ake fama da su, mafi girma sun hada da tsananin talauci da fatara da yunwa da rashin lafiya da rashin tabbas ga rayuwa da rashin tsaro.
Babbar matsala rashin aiki ga matasa harma da ‘yan kasuwa da a kullum suke karyewa suke rasa jari da abin da za su ci da iyalan da suka jima suna tarawa ba tare da tunani za a wayi gari abin da za a ci zai fi karfin su ba.
Sanin kowane ta wannan fanni duk kasar nan babu wanda za ka bashi littafin da ya yi imani da shi na kur’ani ko linjila ya rantse da cewa an cigaba ta wadannan fannoni.
Duk da cewa nasan ko rantsuwa na yi b azan yi kaffarah ba idan da tun farko an ce da mutane za a tsinci kai cikin wannan matsala su zabi wannan gwamnati ta Buhari fiye da rabin masu zabe za su gwammace da duk wani hali da aka samu kai ciki a baya idan ya so mutane su tashi tsaye su nemi hanyar da zasu magance matsalolin ta hanyar yin bore don kawar da gwamnatin ko kuma a shiga rokon Allah babu iyaka har Allah ya kawo gudummowar sa ga lamari. Amma mutane da dama sun yi hakuri sun wakkala lamarin ga Allah da nufin tunanin duk yadda aka je aka dawo za a samu mafita amma yau kusan shekara hudu lamarin kamar karawa ake yi.
Kuma shugabanni har yanzu babu wata magana zaunanniya da akegani za su yi don kawo karshen wahalar da mutane ke sha a kasar nan. Kamar yadda na shafe shekara 32 ina ra’ayin Buhari tun da a ka yi ma sa juyin mulki bayan ya ziyarce mu Ina sakandare a garin Ningi 1985 ya na koma wa a ka tuntsurar da gwamnatinsa.
Tun daga lokacin ya shiga zuciya ta har zuwa shekaru biyu da suka wuce inda a ra’ayina na fahimci akwai gazawa cikin lamarin jagorancinsa na ce a bana yi ina gani ko zaben ban yi zaton zan sake yi ba. Saboda a zaben da ya wuce guri’ata da ta matana hudu nace da a rasa su gwamma na bar duk wani aiki na jarida a ranar zabe kuma haka aka yi tun bakwai na safe na kwashe su zuwa rumfar zabe sai goman dare muka koma gida. Akwai wani jaririna saura kadan ya mutu a firmitsi a bayan mamarsa Allah ya kiyaye aka ceto shi a ka daga sama.
A ra’ayina tunda naga an rufe kasa ba tare da wani shirin tallafar mutane da ke zaune kan iyakoki ba, an ce kowa ya koma gona amma ba abin da mutum zai ci ya je gonar, ga ma’aikata ana ta korar su daga aiki, an kara kudin man fetir, an kashe martabar kudin kasa, saboda kamar yadda na saba a wancan lokaci kafin zuwan wannan gwamnati nakan tafi kasashe irin su Saudi da Dubai da Misiri don harkokin kasuwa da sauran su, amma lalacewar naira daga 190 ta koma dari biyar da ashirin na san mun shiga mawuyacin hali kuma zuwa ko ina ya gagaremu.
Allah marufin asiri shine da Buhari ya tafi jinya mataimakin sa Yemi Osibanjo ya yi tsaiwar daka aka farfado da darajar naira zuwa dari uku da biyar a banki, a kasuwar bayan fage kuma 360 naira a dala daya, shine aka samu sauki. Idan ba domin haka ba wallahi aikin hajjin da ake kuka da sai ya kusan naira milyan uku tunda ana zaton dala daya idan da lamarin ya ci gaba da lalacewa sai naira ta yi lalacewar da za ta kusan naira dubu a dala daya.
Wannan ba karamin bala’i bane irin wannan manufa ta faru a kasar Zimbabwe komai ya lalace kudinsu sai a cika wilbaro a kai bola a zubar saboda haka komai ya gubace sai wahala suke yi tunda suka dauki wasu manufofin tattalin arziki na korar turawa manoma a kasar alhali mutanen su basu iya nomar ba haka suka lalata gonakin su yanzu sun nemi turawan su ma dawo su ci gaba da zama sun ki dawowa.
Kamar haka lamarin ya kasance a Nijeriya inda aka nakasa kudin kasa aka kara farashin mai aka rufe kasa da nufin kowa yayi noma alhali, babu kasar nomar a wasu jihohi irin su Lagos me mutane sama da miliyan goma da su jihohin kudu maso kudu irin su Kalaba da Ribas da sauransu. Hatta Kano kafin mutum ya bar Yakasai da safe ya fita wajen gari zuwa gona rana ta take to ina batun nomar, alhali ba kudi mutum ba shi da sana’a bai ci ya koshi ba.
Kuma magana ta gaskiya duk zancen noma yaudarace saboda a yanzu kasar nan ta wuce nomar fartanya, saboda duk inda su ka cigaba injina su ke girkawa don yin noma yadda za ka ga gonar mutum daya tafi kilomita dari a America ko China ko Jamus.
Kuma idan akwai aikin hankali bai kamata a rufe kasa babu abinci ba ace wai kowa ya je ya yi noma, to wanda bashi da kudin noma ko ba shi da hanyar abinci me ake so ya yi idan ba sata ko barna ko ha’inci ba don ya rayu. Idan noma dadi ne gwamnati ke da filayen noma irin su Hadeja Jamaare riber basin da Chalawa da Shiroro da Bakolori da Kafin Zaki dam da Kumadugu Gana da Dadin kowa a gombe da Benue Riber Basin da Shiroro da Kainji da sauran su, idan nomar sauki ne me yasa gwamnati daga tarayya da jiha da kananan hukumomi ba za su fara bude irin wadannan wurare su kara yawan dam a ko ina suci gaba da noma ba ta hanyar auno taraktoci da kayan feshi da irin zamani da sauran abubuwan da ake bukata don aikin gona ba?
Saboda haka abin da ake wa talakan kasar nan yaudara ce irin ta dan boko yadda duk son addinin mutum bai isa ya rantse ba akan cewa an cigaba cikin wannan gwamnati illa iyaka ya fadi son ransa kurum don son zuciya ko neman abin duniya, don ba wata kasa da ta taba gyaruwa da talauci.
Yawanci maganar mutane shine an samu ingancin tsaro, wannan kuma wani abune da duk wata gwamnati da ta zo ko arnen arewane za a iya samun sa saboda baya cikin ajandarsa ta raba kasar nan kamar yadda ‘yan kudu maso kudu suke da wannan tunanin a kullum. Kamar yadda a lokacin Goodluck ake ganin jirgi mai saukar ungulu na sauka a inda a ke zaton tungar ‘yan boko harm ne, kuma irin su har uku suka yi hatsari a jihohin Borno da Adamawa an samu kudin waje da makamai harma da turawa a Jiragen za su kai wa ‘yan ta’adda amma duk da sanin ko jirgin feshi ya tashi sai da sanin gwamnati, amma har yau saboda munafunci irin na kasar nan babu wanda aka tuhuma ko aka hukunta.
Abin tausayi a wancan lokaci shine yadda idan bom ya tashi za a shiga unguwa a kame matasa a tafi dasu a kashe, a kai hari makarantu da asibitoci da kasuwanni da shaguna da tasohin mota da asibitoci da gidajen masu kudi da bankuna saboda ‘yan kudu a wancan lokacin suna tunanin dukkan gina arewa da aka yi an yi ne da kudin man fetir don haka rigunan wuyan mu da gidajen mu da abubuwan hawan mu duk su na tunanin kudin ruwan fetir ne mu bamu da komai mun zamo kaska mai shan jini don haka ba abin da ya dace illa a gasawa ‘yan arewa aya a hannu yadda su da kansu za su nemi a raba kasar idan mun sha wuya. Amma duk da yunkurin da arewa suka yi wannan gwamnati ta Buhari da ta zo gani ta ke yi a lallabi ‘yan kudu shine mafita yadda za a sake kafa gwamnati ta kowane hali.
Don haka akasarin ayyukan wannan gwamnati an fi yin su a kudancin Nijeriya, yayin da arewa kuma aka shake musu wuya ana musu kanshin mutuwa ta hanyar rufe kan iyakoki yadda mutanen da ke wadannan yankuna a halin yanzu tsananin talauci ya mayar da su barayi da masu garkuwa da mutane ko matsafa ko ‘yan damfara da karuwanci da zinace zinace don neman kudi da sauran ta’addanci yadda an kai wani matsayi da talauci ya fitar da kowa a hankalin sa kullum kara tsiyacewa a ke yi.
Amma duk da irin wariya da rashin adalcin da akewa mutanen arewa har yanzu talakan arewa bai san akwai wata matsala ko cutarwa da gwamnatin Buhari ke yi masa ba, idan ka taba shi zai ce ko zamu ci kasa sai Buhari.
Wasu cewama suke yi ko baba zai daure mu yana harbewane sai shi duk yana yi ne a cikin gyara, wasu ma cewa suke yi ba laifinsa bane na shugabannin bayane tun daga kan su Tafawa Balewa da sojoji da shagari dama basu kafa kasar ba kan tubali mai kyau ba don haka sai yanzu a lokacin Buhari mummunan kafi da mugun tanadi da suka yi har zuwa kan PDP da ta shekara 16 yanzu wahalar ke bayyana amma Baba zai gyara idan ya sake cin zabe.
Sun manta da a baya irin alhairan da aka musu yadda hatta annoba idan ta bayyana haka za a fita a sayo magani a kawo a raba kyauta, yanzu ko sai kungiyoyin duniya irin su Redcross da Unicef ke taimakawa a wannan fannin kuma har yanzu ana musu bita da kulli idan sun ga inda gwamnati ta gaza wajen tallafawa mutanen ta kamar yadda ya faru kwanaki a Borno inda suka samu soja da badakala amma da kungiyoyin su ka fada aka ce su bar kasar an soke ayyukan su, amma washe gari da aka ga ‘yan gudun hijra sun fara bore sun damu aka ce an janye wannan umarni na soja kungiyoyin na duniya suka cigaba da ayyukan taimakon mutane a sansanonin gudun hijra.
Haka yunwa a wancan lokaci idan ta shigo ake sayo abinci a sayar a farashi mai sauki ko a raba kyauta amma yanzu ana kallo sai ko mutane su mutu ko su lalace amma talaka kullum cewa yake sai Baba. Allah ka raba mu da sharrin son maso wani koshin wahala sai wani makon.

Exit mobile version