Daga Mustapha Ibrahim,
Shugaban rukunonin kamfanin Jifatu na Kasa, Alhaji Sabitu Yahaya Jifatu ya bayyana cewa Kaddamar da fara aikin layin aikin dogo na jirgin Kasa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi abin a gode masa ne kuma a yaba masa, domin wannan aiki ne da ake bukatarsa Sama shekaru 1000 da suka wuce idan a kai la’akari da tahiri na shekara aruaru na kasuwanci da ciniki a kasar sahara.
Alhaji sabitu Yahaya, ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan kaddamar da aikin da shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi a Jihar Katsina Larabar da ta gabata.
Alhaji Jifatu ya ce wannan aiki na titin jirgin abu ne da zai kawo bunkasar arziki mai yawa a tsakanin al’ummar Nijeria, musamman Arewa da ita kanta Nijar da ma Kasashen Afrika gaba daya.
Ya ci gaba da bayyana cewa, wannan aiki na layin dogo da hada jahohin Katsina, Jigawa, Biniwe, da sauransu har zuwa Maradi na daruruwan mila milai abu ne da za a iyabcewa naka sai naka, wannan shi ne aikin da Buhari ya yi a wannan lokaci bisa la’akari da cewa ko a zamanin shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ma assamar da kan iyaka da ake kira semi border, to ka ga wannan shi ne aikin dake nuna kishin Arewa.
A karshe Alhaji Sabitu Jifatu ya shawarci aluma kan su bada goyon baya da hadin kai domin samun nasarar wannan aiki wanda matasa ko al
uma da za su zo na gaba su ne za su fi kowa cin gajiwar wannan aiki.