FARFESA HABU MUHAMMAD, fitacce ne a Jami’ar Bayero da ma sauran jami’oin gida da na waje, mutun ne mai kishin ganin an inganta tsarin Dimokuradiyya, da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya baya ga zamowar sa cikin masu kyakyawar fahimta a kan al’adu da harshen Hausa. Watanni biyu da suka gabata, ya zama shugaban cibiyyar nazarin kimiyyar siyasa da ke gidan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano, wanda aka fi sani da Gidan Mumbayya da ke karkashin Jami’ar Bayero ta Kano. Wakilinmu MUSTAPA IBRAHIM KANO ya tattauna da shi kan akidar siyasar Malam Aminu Kano, daya daga cikin mazan jiya ‘yan gwagwarmaya, da kuma ta ‘yan siyasar wannan zamanin. Har ila yau da sauran wasu al’amura da aka bullo da su a cibiyar wanda za a rika gabatarwa da harshen Hausa zalla, ga dai tattaunawar kamar haka:
Da farko za mu so ka gabatar da kanka…
Sunana Farfesa Habu Muhammad, ni ne Babban Darakta ko kuma in ce, Shugaban Cibiyar Nazarin Kimiyyar Siyasa, da ke Gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Gidan Mumbayya, da ke karkashin Jami’ar Bayero ta Kano. Na zama Daraktan wannan cibiya ne a ranar 6 ga Oktoban 2022. Hakan ta kasance ne bayan mutumin da na gada Farfesa Zango ya kammala wa’adin aikinsa na jagorancin gidan da ke Unguwar Gwammaja, a Karamar Hukumar Dala.
Farfesa bari mu dan yi waiwaye adon tafiya, ko za ka dora akidar siyasar Malam Aminu Kano da ta ‘yan siyasar yau a mizani?
To ita siyasa irin ta su Malam Aminu Kano siyasa ce ta a kida ta a `yantar da talaka daga kangin bauta da wulakanci da ake wa talaka a wancan lokacin, kuma siyasa ce ta neman `yanci domin sun san, ko mene ne ‘yanci domin ko ba komai sun yi gwagwarmaya da gumurzu na shan wahala da suka samu daga turawan mulkin mallaka kan maganar `yanci. To ka ga wasu daga cinkin su ko su Malam Aminu Kano suna da wannann ilimin kuma suna da wannan ruhin na neman `yanci cikin wahala da azaba da matsaloli daban-daban.
Saboda haka za ka ga siyasar su Malam Aminu Kano siyasa ce ta neman `yancin talaka, da `yantar da shi daga kangin bauta da za ka iya cewa masu gudanar da mulki na wancan lokacin sun sa talaka a kangin bauta, haka ne ma ya sa su Malam Aminu Kano da sauran `yan siyasar zamaninsa suke da wani take na SAWABA-SAWABA, to abin da suke nufi a wancan lokacin nasu shi ne irin abin da suke wa talaka na karbar haraji, da jangali, da sa mutum noma a gonar Rogo, ko makamancin haka ba tare da an biya shi ba, to wannan da wasu abu masu kama da wannan shi ne abin da su Malam Aminu Kano suka yi yaki da shi a tafiyarsu ta NEPU da PRP kuma wannan za ka ga cewa ita ce a kidar su Malam Aminu Kano da sauransu.
Kuma har ila yau wani abin lura, su, su Malam Aminu Kano babu batun tara kudi a akidar su illa dai kawai `yancin talaka, da biya masa bukata daidai gwargwadon iko, ka ga babu maganar cin hanci da rashawa da almundahana amma na yanzu mafiyawa daga cikinsu ko 99 bisa 100 suna kokarin tara abin duniya ne har ma ya fi karfin bukatarsu ta rayuwa. To saboda haka a takaice akidar siyasar Malam Aminu Kano ta sha bamban nesa ba kusa ba da `yan siyasarmu na yau.
Bambanci ko kuma in ka kwatanta da `yan siyasar yanzu a kasin haka ne, wato su ‘yan siyasar yanzu ba su san ma mene ne `yanci ba, abin da suka sani shi ne tara kudi dan amfanin kansu da `ya`yansu, da matansu, da wadanda suke so su azurta, saboda haka idan ka kwatanta siyasar su Malam Aminu Kano da `yan siyasar yau abin ya sha bamban nesa ba kusa ba saboda canjin zamani da canjin yanayin.
Farfesa, wacce rawa jaridun Hausa za su taka wajen samun nasarar wadannan sabbin tsare-tsare?
To bisa la’akari da yadda muka lura da cewa kafofin yada labarai na Hausa da jaridun Hausa suna da dinbim makaranta da masu bibiyarsu babu shakka, haka za mu hada kai da Jaridun Hausa sosai domin isar da sako a lungu na birni da karkara, ba ma kamar mutanenmu da suke kudancin kasar nan da ma sauran wasu wurare suna bibiyar jaridun Hausa da sauransu. Yanzu ana bibiyarmu ma ta hanyar kafofin sadarwa na zamani, to wannan abu ne da za mu yi iya kokarinmu mu ga mun hada kai da duk wata kafa da sakonmu zai isa duk inda ake bukata gwargwadon hali.
Ana yin hakan ne domin al’umma su rika samu suna karantawa a kokarin da muke na wayar da kan al’umma ta kowanne fanni, har ma da abubuwan da suka shafi turanci shi ma sai an yi da shi, duk da yake mu dai burinmu shi ne masu jin Hausa a ba su damarsu ta karantawa da Hausa da kuma saurare da sauransu, burinmu dai shi ne mu ilmantar da al’umma masu jin Turanci da masu jin Hausa zalla, a wannan cibiya ta nazarin kimiyyar siyasa ta Gidan Mumbayya.
Haka nan muna da dangantaka ko alaka kyakkyawa da kafofin yada labarai na Talbijin, da Rediyo dake nan Kano da muke gabatar da shirye-shirye, a kullum so ake a fadi wani abu domin yada ilimi cikin duniya ta wadanan kafofi.