Daga Mustapha Ibrahim Tela, Kano
Daya daga cikin mashahuran dattawan Nijeriya kuma mai fashin baki kan al’amuran siyasa Dattijo mai shekara sama da 90 a duniya Alhaji Tanko Yasakai ya bayyana cewa duk mai son gyaran tsarin Najeriya, to ya dace da ya bayyanawa al’umma Nijeriya yaya gyaran tsarin Najeriya ya ke, ya kuma ya ke so Nijeriya ta kasance, domin mafiya yawa ‘yan Najeriya ciki har da ni Alhaji Tanko Yakasai bamu san, me ake nufi da gyaran tsarin Nijeriya ba, don haka duk mai so ya bayyana yadda abin yake, ta haka ne za’a goyi bayan sa, ko aki goyan bayansa, gwargwadan ra’ayin ko wanne dan Nijeriya.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Tanko Yakasai tsohon kwamishinan yada labarai na Jihar kano kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara, a lokacin da yake ganawa da wakilin Jaridar Leadership A Yau a gidan sa da ke birnin kano, a ranar da ta gabata ,yace sau da yawa za ka ji mutum yace yana goyan bayan tsarin Najeriya, to sai ka yi tsanmanin ko ya san abin da ake nufi ne, amma idan ka bi a hankali sai ka ga ya gaza yin cikakken bayani, akan gyaran tsarin zaman Nijeriya, sai ka ji ya ce akwai tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da kuma tsohon maitaimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da su ka yi magana ta goyan bayan gyara tsarin zaman Nijeriya a madauri daya, to sai na yi tsanmanin za su yi bayanin me nene katamaimai wannan tsarin ya ke nufi, amma sai su kasa yin wani bayani, don haka muna sauraran mu ji hakikanin abin da ake nufi mutum ya goyi bayan haka, ko ya ki a cewar daya daga cikin dattawan Nijeriya.
Haka kuma ya bayyana wata magana ta tsayawar takara a kashin kanka ba karkashin wata Jam’iya ba, da cewa abu ne mai kyau indai ya samu inganci, kuma ya samu karbuwa domin yin haka zai hana Jam’iyyu kama karya da murde dan takara mai nagarta,wanda Jam’iyya bata so wannan dama ce idan mutum ya samu matsala da Jam’iyya, to abu ne mai sauki ya dawo ya tsaya da kafar sa, idan mutane sun gamsu da nagartassa sai su zabe shi, ita kuma Jam’iyya ba ruwan ta, to wannan zai gyara siyaysar Njeriya don haka abu ne mai kyau da wannan tsari da majalisa ta yi a halin yanzu.