Shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al Bashir ya bukaci mazauna yankin Darfur da suka tsere daga gidajensu, su koma gida sakamakon kawo karshen yakin da aka gwabza wanda hallaka dubban mutane.
Akalla mutane sama da miliyan biyu da rabi ne suka tsere daga yankin na Darfur, sakamakon tashin hankalin da ya barke cikin shekara ta 2003, lokacin da ‘yan tawayen daga kananan kabilun yankin suka fara yakar sojojin kasar, bisa zargin kuntatawa yankin ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki.
Akasarin mutanen da suka tsere sun samu mafaka ne a sansanonin ‘yan gudun hijira, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda aka hallaka sun kai akalla 300,000.
Yayin ziyarar da ya kai zuwa ankin na Darfur, shugaba Omar al Bashir ya sanar da kawo karshen yakin da aka kwashe tsawon lokaci ana fafata shi.
Kokarin da al-Bashir ya yi na kawo karshen dadadden yakin, bangare ne mai muhimmanci daga cikin sharuddan da Amurka ta gindaya masa kafin cire takunkumin karya tattalin arzikin da ta kakaba masa.