A lokacin bincikenmu da muka gudanar a wani kauyen da ake kira da ‘KAHUTU’ dake karkashin kulawar garin Dabai a Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina a shekarar 2016 mun ci karo da abubuwan tarihi da suka hada da; kushewar bawan Allah, takun giwa (mai kofatai), matattarar ruwa, kaburbura, da sauran su.
Mai Kofatai: Ana kiran wannan dutsen ne da ‘TAKUN GIWA’ ko kuma ‘MAI KOFATAI’, wurin na cikin kauyen Kahutu. Tarihi ya nuna cewa; a da kafin yanzu, namun daji ne iri-iri suke zuwa wurin suna hawa dutsen suna hutawa. Sakamakon yawan hawa wurin da dabbobin suke yi ya sa idan ka zo dutsen zaka ga sahun dabbobi iri-iri. Har yanzu wurin yana nan, sai dai sawayen ya fara dusashewa. Amma kana iya ganin wasu alamu na sawaye a cikin dutsen da suke da daukar hankali.
Matattarar Ruwa: Idan ka isa wurin, zaka tarar da wani rami ne wanda ya kai tsawon mita 728. Tarihi ya nuna cewa; an yi wani bawan Allah ne da ake yi wa lakabi da Waliy Muhammad Nakahutu, a lokacin da ya rasu mutane sun hadu bayan an haka kabarinsa a kusa da wani dutse, isar wurin ke da wuya da nufin bizne shi, sai aka tarar ruwa ya cika ramin da aka haka domin bizne shi, daga nan sai mutanen suka fasa bizne shi a wurin, suka haka wani rami a gefen wannan ramin sannan suka bizne wannan bawan Allah.
Tun daga lokacin, mutanen kauyen sun tabbatar mana da cewa; ramin ya rika rike ruwa da tara shi har na tsawon shekara, wanda wannan ya sa mutanen kauyen ke amfana da shi. Sannan a cewarsu; a da (banda yanzu) wurin ya rika yin haske musamman a daren Juma’a. Daga nesa kana ganin haskensa fau kamar hasken farin wata.
An zagaye su, kuma har yanzu akwai masu ziyarar kabarin na su. Wani abin mamaki shi ne; masu ziyarar idan suka zo suna ajiye kudi domin neman tabarruki a kasan dutsen duka kaburburan na su. Idan ka daga dutsen sai ka ga tarar da kudi. Ni ma shaida ne, domin na tsinci kudi, na dauka na kuma kashe. An sakawa wannan wuri suna da ‘KUSHEWAR BAWAN ALLAH’ ne sakamakon kaburburan wadannan bayin Allah da yake wurin, kuma ya zama ana girmama su. Kafin rasuwar Waliy Muhammad Nakahutu akwai wata bishiyar tsamiya da ya kasance yana zama karkashinta domin hutawa. Sannan haka zalika har yanzu akwai shaidar Masallaci da ya yi yana gabatar da Sallah a wurin sallah.
Mun tattaro muku wannan labari daga Shafin Rariya.