Alhazan Kaduna 2,842 Sun Dawo

Daga Abubakar Abba, Kaduna

Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, Alhazan jihar dubu 2,842 ne suka dawo gida daga kasar Saudiyya.

Kakakin Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, Yunusa Abdullahi, ya shaidawa wakilinmu hakan ta wayar tarho.

Ya ce, alhazan an dawo da su ne a jirgen ‘Medbiew’ da ‘Mad Air’ a jigila ta shida. Ya kara da cewa, Medbiew ya dawo da Alhazai su 1,786, jirgin Mad Air kuma ya dawo da Alhazai 1,078.

Ya kara jaddada cewa za a kwaso dukkan Alhazan kamar yadda aka tsara. Adadin alhazai  6,713 ne suka sauke farali daga jihar ta Kaduna a aikin hajji na shekarar 2017.

Exit mobile version