ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Allah Ya Daukaka Ambaton Manzon Allah (SAW) A Duniya Da Lahira

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 years ago
Manzon Allah

Har yanzu dai muna nan a cikin bayanin irin yabon da Allah (SWT) ya yi wa Annabi (SAW) a cikin Alam nash’rah, ayar da ta ce “mun daukaka ambaton ka”, wato aya ta 4 a cikin surar.

Sahabin Annabi (SAW) Katadatu (RA) ya ce, “Allah ya daukaka ambaton Annabi (SAW) a cikin duniya da kuma lahira. Babu wani mai yin huduba ko mai shaidawa ko sallah face yana fadin cewa na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Ma’aikin Allah ne”. Ma’ana a nan, Allah ya daukaka ambaton Annabi ta yadda idan aka fadi sunansa sai a fadi na Annabi (SAW).

  • Sin Ta Sha Alwashin Hadin Gwiwa Da Sauran Sassa Wajen Dakile Tashin Hankali A Tekun Red Sea
  • Yadda ANA Ta Shugabanci Gangamin Saukaka Zuwa Hajjin 2024 A Nijeriya

Abu Sa’idul Kudri (RA), Sahabin Annabi kuma Dan Badar ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce “Jibrilu (AS) ya zo mun sai ya ce, Ubangijina kuma Ubangijinka – ya Muhammad – yana cewa shin ka san ma’anar fassarar ayar da ta ce Allah ya daukaka ambatonka? Sai na ce Allah ne da Dan Aikensa (Jibrilu) ya sani. Sai Jibrilu ya ce ma’anar an daukaka ambatonka ita ce Allah ya ce idan aka ambace shi sai a ambace ka tare da shi”.

ADVERTISEMENT

Ibn Ada’in ya ce ma’anar “mun daukaka ambatonka” tana nufin “Allah ya sanya ambatonsa tare da ambaton Annabi ya zama cikar imani”. Wato idan aka ce “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah”, imani ba zai cika ba dole sai an hada da “Hakika na shaida Muhammadu Manzon Allah ne, (SAW)”.

Ko kuma Ibn Ada’in ya ce a wata ma’anar, ayar tana nufin “Allah ya sanya ambaton Manzon Allah a matsayin ambatonsa”. Wato duk wanda ya ambaci Manzon Allah (Muhammadu) tamkar ya ambaci Allah ne.
Shi ya sa ma wasu Malamai suka ce sunan “Muhammadu” daya ne daga cikin sunayen Allah da ya baiwa Annabi (SAW), kamar yadda ya bashi “Ra’ufu” da “Rahimu”.

LABARAI MASU NASABA

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

A wurin Imamu Ja’afarus Sadik (RA) kuma, ma’anar ayar ta “mun daukaka ambatonka tana nufin “Babu wani mutum da zai ambaci Manzon Allah (SAW) da Manzanci face sai ya ambaci Allah, duk kuwa da cewa Allah ne Ubangiji”.

A bangaren wasu malamai kuwa, sun yi nuni da ma’anar ayar zuwa mukamin ceto a ranar Alkiyama. Ranar da kowa zai ce takaina nake yi, sai shi kadai (SAW) zai tashi ya nemi ceto a wurin Allah ya bashi. Kowa sai ya ambace shi a ranar, da Annabawa da mabiyansu kowa zai gaza, Annabi (SAW) kadai ne zai iya. Shi ya sa kowa za a ji yana kiran sunansa (Muhammadu, Muhammadu don godewa) har ma Allah a cikin Alkur’ani yake cewa “Allah zai tsayar da kai a wani bigire abin godewa”.

Haka nan, yana daga daukaka ambaton Annabi (SAW) da Allah ya yi, sa’ilin da ya gwama (hada) bin Manzon Allah a matsayin bin sa (SWT). Allah ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW).
Allah yana cewa a cikin Alkur’ani “Ku bi Allah ku bi Manzon Allah daidai-da-daidai (kamar yadda ma’anar wawun na ayar ta nuna)”. A wata ayar kuma ya ce “Ku yi Imani da Allah ku yi Imani da Ma’aikinsa daidai-da-daidai (ita ma wawun din ayar irin ta ayar baya ce, wato ta adafi)”.

Malamai sun ce bai halatta a hada irin wannan magana ba in ba a cikin hakkin Manzon Allah (SAW) ba. Shi kuma tunda Allah ne da kansa ya yi hakan, waye ya isa ya cire?
Malam Alkadiy Iyal ya kawo hadisi wanda ruwayarsa ta daukaka zuwa Sahabin Annabi Khuzaifatul Yamaniy (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce “Kar in ji wani dayanku ya ce Allah ya so (wani abu); wane ya so (shi ma, wato a sanya harafin wawun da ke nuna daidai-da-daidai), sai dai mutum ya ce Allah ya so; sannan wane ya so (ma’ana sai da Allah ya so, sannan daga baya wane ya so, ba tare da daidaitawa”. A ka’idar Larabci ba za a yi amfani da “wawun na adafi” ba sai dai harafin “summa”.

Malam Khaddabi ya ce Annabi (SAW) ya shiryar da Sahabbai yin ladabi ga Allah ta yadda sai an gabatar da son Allah sannan a gabatar da son wani (Kamar yadda ya zo a bayanin da muka yi a sama), don haka ne Annabi ya zabar musu amfani da “summa” ma’ana “sannan ko daga baya” domin jera magana da jinkirtawa. Wato sai an fadi na Allah, sannan daga baya a fadi na Bawansa.

Ya zo a wani Hadisi cewa wani mai huduba ya mike a gaban Annabi (SAW) zai yi huduba sai ya ce “Duk wanda ya bi Allah da Ma’aikinsa; ya shiryu, wanda ya saba musu su biyu kuma…” daga nan Annabi (SAW) ya ce “Tir da mai yi ma mutane huduba irin ka, tashi ka tafi”, ma’ana mai hudubar bai iya magana ba.

Abu Sulaiman ya ce Annabi (SAW) ya kyamaci hada sunayen guda biyu (na Allah da nasa) ne da harafin kinaya (jirwaye mai kaman wanka). Amma wani Malamin ya ce ba haka ake nufi ba, ya ce Annabi ya hana ne saboda mai hudubar ya yi wakafi a wurin. Sai dai kuma fahimtar Abu Sulaiman ta fi inganta saboda abin da aka ruwaito a Hadisi Sahihi shi ne mai hudubar bai yi wakafi ba a wurin harafin na kinaya (jirwaye), ya cike maganarsa inda ya ce “wanda ya saba musu su biyu ya halaka”.

Shi kuwa Imamun Nawawi ya ce duk ba haka ba ne. Ya ce sababin da ya sa Annabi (SAW) ya hana irin wannan hadawar saboda a huduba ne ya fada, kuma ita huduba ana so ne a fadi ma’ana wara-wara yadda za a fahimta filla-filla ba a yi kinaya ba. Shi ya sa Annabi (SAW) idan ya fadi wata magana sai ya maimaita don a gane. Amma ba wai ya ki a hada sunayen guda biyu (na Allah da nasa) ba ne. Domin hakan ya zo a cikin Alkur’ani da Hadisi.
Malaman Tafsiri sun yi sabani cikin ma’anar ayar da ke cewa “Allah da Mala’ikunsa “suna” yiwa Annabi salati…”, shin ma’anar “suna salatin” za ta zama a hada Allah Tabaraka Wa Ta’ala da Mala’iku ne cikin yin salatin ko kuma ayar ana kaddarata ce da ma’anar “Allah Yana salati”, “Mala’iku (su ma) suna salati”?.

Wane sashe na malamai sun tafi a kan “Allah Yana salati, Mala’iku suna salati ga Annabi…”, wasu kuma sun kyamaci a ce hakan. Sai suka kaddara fi’ilin (aiki) na “suna” ga Mala’iku bayan sun gabatar da Allah shi kadai Yana salatin a matsayin abin kaddarawa cikin “Yusalluu”, mana “suna”. Alkur’ani yakan kawo irin wannan abin kaddarawan.
To duk fahimtar da mutum ya dauka dai a cikin wadannan ya yi daidai.
Ba gyaran akida ba ne a rika cewa kar a rika ambaton Allah tare da Annabi, a’a, imani ma ba zai cika ba sai an ambaci Allah tare da Annabi (SAW). Shi ya sa ma idan ana neman wani abu ake cewa “don Allah don Manzon Allah”.
An karbo daga Sayyidina Umar bin Khaddab (RA) cewa wata rana yana hira da Manzon Allah (SAW) sai ya ce masa “yana daga fifikonka ya Rasulallahi a wurin Allah, Allah ya sanya bin ka; bin sa ne”.

Allah (SWT) a cikin Alkur’ani, Suratun Nisa’i ya ce “duk wanda ya bi wannan Ma’aiki, ya bi Allah”. A cikin Suratu Ali Imran kuma ya ce “Ka fada musu – ya Rasulallah – in dai kuna son Allah; to ku bi ni sai Allah ya so ku”.
An ruwaito cewa a yayin da wannan ayar ta Ali Imran ta sauka, Kafirai sun ce “Muhammadu yana so ne mutanensa su rike shi Badade kamar yadda Nasara suka riki Isah”. Sai Allah ya saukar da wannan ayar “Gaya musu – ya Rasulallah – ku bi Allah ku bi Ma’aiki (daidai da daidai)”. Allah sai ya daidaita binsa da bin Manzon Allah (SAW) domin ya durmuza hancin Kafiran.

Don haka a cikin addininmu idan Allah ya halatta mana yin abu, don an samu wasu mutanen da ba Musulmi ba suna yi, ba za a kula da su ba ballantana har mutum ya ji shakkun cewa ai tunda wadancan suna yi bai kamata muma mu yi ba. Idan addininmu na Musulunci ya yarda a yi wani abu, to koda Nasara ko Yahudu suna yi; babu ruwanmu da su; ba nasu muke yi ba, na Musulunci muke yi.

manzon Allah
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

MASU ALAKA

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Next Post
Nijeriya

Burikan ‘Yan Nijeriya A 2024

LABARAI MASU NASABA

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.