ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Al’ummun Duniya Sun Dora Muhimmanci Ga Tattaunawar Shugabannin Sin Da Amurka

by Sulaiman
4 months ago
Sin

Da safiyar jiya Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.

Shugabannin biyu sun shafe sa’o’i 2 da mintuna 15 suna zantawa. Kuma yayin tattaunawar, shugaba Xi da shugaba Trump, sun amince da kafa “dangantaka mai dorewa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Amurka”, a matsayin sabon matakin inganta dangantakar kasashen biyu.Wannan mataki zai zamo jagora bisa hangen nesa ga dangantakarsu cikin shekaru 3 masu zuwa, har ma da makoma ta dogon lokaci.

Kana an yi imanin cewa, hakan zai samu karbuwa daga al’ummomin kasashen biyu da ma al’ummun duniya baki daya.Al’ummar duniya na mayar da hankali sosai ga tattaunawar shugabannin biyu.

ADVERTISEMENT

Mutane da yawa daga kasashen duniya suna ganin cewa, wannan tattaunawa na da muhimmanci matuka a tarihi, kuma ta aike da sako mai kyau ga duniya.Game da hakan, masanin harkokin gabashin Asiya na Amurka, kuma malami mai ziyara a jami’ar Fairleigh Dickinson Jesse P Gates, ya ce a yayin tattaunawar, Shugaba Xi ya sake kimanta dangantakar Sin da Amurka da wani babban jirgin ruwa, wato ana bukatar bangarorin biyu da su yi tafiya tare a cikin wannan jirgi, domin inganta hadin gwiwarsu yadda ya kamata. Gina “dangantaka mai dorewa bisa manyan tsare-tsare na kasashen biyu” shi ne zabin da ya kamata a yi don ci gaban kasashen biyu, kuma tafiya tare tsakaninsu, ba ma kawai zai amfani kasashen biyu ba ne, har ma da duniya baki daya.

A nasa bangare, shugaban jam’iyyar ‘yan kasa ta Australiya ACP Robert Barwick, ya ce abubuwan da shugaba Xi ya fada a yayin tattaunawar suna da ma’ana sosai kuma suna da ban sha’awa.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Shi kuwa tsohon ministan harkokin wajen kasar Ecuador, kuma tsohon shugaban babban taron MDD Maria Fernanda Espinosa Garcés, cewa ya yi wannan tattaunawa ta shugabannin Sin da Amurka, tana da babban muhimmanci a tarihi, kuma abokantaka da hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen Sin da Amurka, na iya ba da gudunmawa mai yawa ga bil’adama. (Amina Xu)

Sin
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Sin

2027: Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Matashin Dan Siyasa ‘Al’ajabin Zazzau’

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.