ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Matashin Dan Siyasa ‘Al’ajabin Zazzau’

by Sani Anwar
4 months ago
Siyasa

Mahmud Sadis Buba mai shekaru 30 ya jawo hankula sosai tun bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar mazabar tarayya ta Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Matashin zai fafata neman tikitin jam’iyyar APC da dan majalisa mai ci, Sadik Ango Abdullahi, dan fitaccen dattijon kasa, Farfesa Ango Abdullahi.

Buba, wanda aka fi sani da lakabin “Al-ajabin Zazzau” saboda karfinsa da girmansa, ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen mazabar, inda masu bibiyar siyasa da dama ke sa ido kan yadda tasirinsa ke karuwa.

ADVERTISEMENT

Mazabar tarayya ta Sabon Gari ana kallonta a matsayin daya daga cikin mazabu mafi tsananin gasa a siyasar Jihar Kaduna. Mazabar na da fitattun ‘yan siyasa da suka hada da Mataimakin Shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Garba Datti Babawo; tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali; da tsohon Shugaban PDP na Jihar Kaduna, Sa’in Jama’a.

Mazabar, wadda ta kunshi gundumomi 13, tana dauke da cibiyoyin gwamnatin tarayya da dama tare da al’umma mabambanta, abin da ke sanya fafatawa a zaben ke zama mai zafi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Buba, wanda ke zaune tare da iyayensa a Layin Ambassador da ke Samaru a Zariya, bai yi aure ba kuma sabo ne a harkar neman mukamin zabe.

Yayin da wasu ‘yan siyasa da farko suka dauki aniyarsa a matsayin neman suna kawai, wasu yanzu suna kallonsa a matsayin babban dan takara saboda alakarsa da manyan ‘yan siyasa a matakin jiha da na kasa.

Wasu daga cikin magoya bayan dan majalisa mai ci, Sadik Ango Abdullahi, na kallon shigar Buba cikin takarar a matsayin wasan kwaikwayo kawai da kuma yunkurin neman suna a yankin.

Wani magoyin bayan APC a Samaru, Malam Ali “Go Slow,” ya bayyana Buba a matsayin matashin mai iya tara jama’a, wanda a baya ya rike mukamin shugaban kungiyar goyon bayan “Tinubu–Uba Sani Agenda 2027.”

Ya ce kuruciyar kamannin Buba ta haifar da ce-ce-ku-ce sosai a kafofin sada zumunta bayan hotuna da bidiyon tantancewarsa a Abuja sun bazu.

“‘Yan Nijeriya da dama sun yi mamakin yadda yake kama da karamin yaro duk da cewa yana neman kujerar Majalisar Tarayya. Wasu ma suna bayyana shi a matsayin daya daga cikin matasa mafi kankanta masu neman takara,” in ji shi.

Ali ya kara da cewa Buba ya gaji tasirin siyasa daga danginsu, domin mahaifinsa na da alaka da tsohon jakadan Nijeriya a Senegal, Amb. Sule Buba.

Bincike ya kuma nuna cewa dan takarar ya kulla alaka da manyan ‘yan siyasa a kasar nan, inda aka gan shi a hotuna tare da Shugaba Bola Tinubu, Gwamna Uba Sani, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da sauran manyan shugabanni na kasa.

An ce ya fara jan hankalin jama’a ne jim kadan bayan zaben 2023 lokacin da hotunansa tare da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari suka bayyana a kafofin sada zumunta.

Wani mazaunin Samaru, Idris Umar, ya tunatar da cewa Buba ya raba buhunan shinkafa ga mazauna yankin a lokacin azumin Ramadan a matsayin wani bangare na ayyukan jin kai da yake yi.

“Duk da irin girmansa da karfinsa, mutane da dama a nan suna sonsa saboda ayyukan taimakon jama’a da yake yi. Amma kayar da dan majalisa mai ci ba zai kasance mai sauki ba domin yana da tushe sosai a siyasa,” in ji Umar.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa dan majalisa mai ci, Sadik Ango Abdullahi, har yanzu yana da gagarumin goyon bayan jama’a, musamman ganin yadda ya lashe zaben fidda gwani na PDP yana cikin hannun masu garkuwa da mutane, sannan ya lashe babban zaben 2023 da rinjaye mai yawa.

Ana kuma ganin dan majalisar mai ci na cin gajiyar tasirin siyasar mahaifinsa, Farfesa Ango Abdullahi, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a Jihar Kaduna, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron abinci, kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa ta Northern Elders Forum a yanzu.

Sai dai masu nazarin siyasa na cewa Buba na wakiltar sabon karni na matasa masu alakar siyasa da ke neman karin damar shiga shugabanci da gudanar da mulki.

Gabatar da takardun neman takararsa da ya yi ga Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Seyi Tinubu, da sauran manyan ‘yan siyasa ya kara jawo hasashe kan yadda tasirinsa ke karuwa a cikin APC.

Magoya bayansa na bayyana shi a matsayin matashi mai kuzari kuma mai kusanci da talakawa, yayin da wasu ke kallon fitowarsa a matsayin alamar karuwar shigar matasa cikin siyasar Nijeriya.

Sun ce idan Buba ya samu tikitin APC sannan ya lashe zaben, zai iya zama daya daga cikin mafi kankantar shekaru a Majalisar Dokoki ta 11 ta Nijeriya.

Martani dai na ci gaba da yawo a kafofin sada zumunta kan aniyarsa, inda mutane da dama ke bayyana shi a matsayin sabon fuska a siyasa.

Idan Buba ya kai ga shiga Majalisar Wakilai, ba zai zama mafi karancin shekaru a wannan zamani ba, domin Ibrahim Bello Mohammed, mai wakiltar mazabar tarayya ta Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza a Jihar Kebbi, ya hau kujerar majalisa a shekarar 2023 yana da shekaru 27 kacal.

Siyasa
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
NJC Ya Dakatar Da Alƙalan Kotuna 2, Ta Ƙara Wa Wasu 12 Girma

NJC Ya Dakatar Da Alƙalan Kotuna 2, Ta Ƙara Wa Wasu 12 Girma

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.