Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kai dauki ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
‘Yan majalisar sun yi wannan kiran ne a zaman da suka yi a ranar Litinin, wanda shugaban majalisar, Hamisu Chidari ya jagoranta.
- Bikin Tsakiyar Kaka Na 2022 Da CMG Ya Nuna Ya Samu Yabo Sosai Daga Masu Kallo A Gida Da Waje
- Kashi 78 Na Dalibai Sun Ci Jarrabawar NBAIS Ta 2022 – Farfesa Shafi’u
Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri kan al’amuran hadin gwiwa da suka shafi rayuwar jama’a cikin gaggawa da ‘yan mazabar Kiru, Bebeji da Rano suka gabatar.
Mataimakin shugaban majalisar kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Kiru, Kabiru Dashi ne, ya gabatar wa da majalisar.
‘Yan majalisar sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi kira ga hukumar raya kogin Hadejia da Jama’are da gwamnatin tarayya da su gaggauta magance kwararar ruwa daga madatsar ruwa ta Tiga.
A cewarsu, yin hakan zai kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa da asarar rayuka da dukiyoyi a yankin.
‘Yan majalisar sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici da bakin ciki, yayin da suka kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya da su kawo dauki ga al’umma.
Bayan tattaunawa ne majalisar ta amince da kudirorin, inda ta jajanta wa al’ummar da abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya kare afkuwar wannan lamari.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa ambaliyar ruwa ta Tiga a makon jiya ta yi barna tare da lalata gonaki da tituna da gidaje da kuma raba mazauna yankunan da muhallansu.
A halin da ake ciki, majalisar ta samu takarda daga gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje na neman amincewar nadin shugaban majalisar tare da sake nada wasu mutane biyar na kwamitin gyaran doka na jihar.
Hukumar Gyaran Shari’a ta kunshi Mai Shari’a Lawan Wada mai ritaya a matsayin shugaba, sai Sadiq Garba, Muhd, Aliyu, Yahaya Rimi, Dakta Muhammad Minjibir, Garzali Zubairu da Hauwa Yusuf a matsayin mambobi.
Wasikar dai an mika ta ne ga kwamitin shari’a na majalisar kuma an ba shi mako guda ya ba da rahoto don ci gaba da ayyukan majalisa.