Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), ta tabbatar da mutuwar mutane 49 a yankuna 226 sakamakon ambaliyar ruwa da iska mai karfi a kananan hukumomi 27 tun daga watan Janairu 2024.
Sakataren Hukumar, Isyaku Abdullahi Kubarachi ne, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Kano a ranar Laraba.
- Hasashen Ambaliya: Gwamna Nasir Ya Kafa Kwamitin Daukar Matakin Gaggawa A Kebbi
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi A Kano
Ya bayyana cewa Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET), ta yi hasashen ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 14, amma Iftila’in ya shafi wurare fiye da haka.
Ya ce yankunan da abin ya shafa da sun hada da Tudun Wada, Gwale, Wudil, Danbatta, Ajingi, Dala, Gwarzo, Madobi, Bichi, Kano Municipal, Karaye, Tarauni, Minjibir, Bebeji, Rogo, Shanono, Kabo, Garin Malam, da Ungogo.
Sauran sun hada da Kumbotso, Nassarawa, Kura, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Gezawa, Rogo da Bagwai.
“Ambaliyar ta lalata gidaje 6,583 tare da shafar mutum 38,814 a fadin jihar. Kazalika, gonaki 8,289 da ke da fadin eka 36,265 sun lalace. Iftila’in ya tilasta wa mutum 1,414 yin hijira, ya jikkata 139, kuma ya kashe mutum 49,” in ji Kubarachi.
SEMA tare da hadin gwiwar wasu hukumomi sun raba kayan agaji domin rage radadi ga wadanda abin ya shafa.
Hukumar ta kuma shirya tarukan bita don hana afkuwar irin wannan Iftila’i a gaba.
Kubarachi, ya gode wa Gwamna Abba Yusuf bisa goyon bayansa ta wajen samar da kayan aiki da sauran abubuwan da suka taimaka wajen daukar matakin gaggawa.
Ya yi gargadi ga al’ummar jihar da su guji gine-gine a kan magudanan ruwa kuma su tabbatar da tsaftace magudanan don rage hatsarin ambaliyar ruwa.