Tare da Baƙir Muhammad
A na sa ran daga nan zuwa shekarar 2020 adaɗin masu amfani da intanet zai ƙaru sosai a Nijeriya, yawan masu amfani da manyan wayoyin hannu, da kallon bidiyo ta intanet, da kuma ƙarfin intanet ɗin daga 3G zuwa 4G zai sa adadin masu amfani da intanet ya ninku har ninki takwas a ‘yan shekaru masu zuwa.
Kamfani intanet mai suna Cisco Networking ya ce ana sa ran mutum miliyan 5.5 ne zasu dinga amfani da wayoyin hannu a shekarar 2020, don haka amfani da intanet zai ƙaru sosai, wannan zai zama ya ninka ƙaruwar shekara biyar ɗin baya.
A Nijeriya kaɗai za’a samu ƙaruwa ta kashi 36 cikin ɗari, saboda a kullum yawan masu amfani da wayoyin hannu na matuƙar daɗuwa, a yanzu haka ana ganin aƙalla sama da layukan waya miliyan 150 ne suke aiki a Nijeriya, wanda haka yasa ake ganin nan da ‘yan shekaru kadan adaɗin zai wuce haka.
Kallon bidiyo a intanet shi ne abin da zai fi yawaita a cikin duk abubuwa da suke amfani da intanet, masu amfani da intanet suna ƙara buƙatar hoton bidiyo mai kyawun gaske, da kuma saurin sauke bidiyon ba latti, don haka dole buƙatar amfani da intanet mai ƙarfi ya ƙaru, intanet mai ƙarfin 4G shine zai maye gurbin masu ƙarfin 2G da 3G da aka saba amfani da su a baya.
Kamfanin y ace adaɗin masu buƙatar intanet na ƙaruwa ko da yaushe, kamar dai yadda masu amfani da wayoyin hannu suke daɗa karuwa a kullum, nan gaba dole a ƙara fito da fasahohi kamar su 5G da Wi-Fi domin magance yawan buƙatar intanet da ke matuƙar ƙaruwa kullum, hakan kuma bna ƙaramin taimakawa al’umma zai yi ba musamman a bangare rayuwar yau da kullum da kuma kasuwanci.