Umar A Hunkuyi" />

Amfani Da Tsabar Kudi Ya Ragu Da Naira Bilyan 75 Cikin Wata Guda

Kudaden da ke yawo a hannun mutane sun ragu da Naira bilyan 75.84, daga Naira tiriliyan 1.9 a watan Yuni zuwa Naira tiriliyan 1.824 a watan Yuli na shekarar 2018.

A bisa kididdigan da ta fito daga babban bankin kasa a ranar Laraba, wannan kididdigan ta taso ne daga Naira tiriliyon 1.93 a watan Fabrairu zuwa Naira tiriliyon 2.03 a watan Maris.

Babban bankin na kasar nan, ya bayyana cewa kudaden da ke kewayawan a hannun mutane sun ragu daga Naira tiriliyon 1.95 da Naira tiriliyon, 1.93 a watannin Afrilu da kuma na Mayu, bi-da-bi.

Da yake magana a kan abubuwan da za su iya shafan jujjuyawan kudaden a hannun jama’a, shugaban sashen tattalin arziki da makamantansa na bankin, Dakta Ayo Teriba cewa ya yi, dalili guda shi ne, karuwar yin cinikayya da manhajojin yanar gizo wajen saye da sayarwa, kamar karuwar mashinan ATM, da manhajojin siye da sayarwa na PoS, da hanyoyin yin musayar kudi ba tare da yin amfani da takardun kudade din ba.

Ya ce, a yanzun babu bukatar ka cika aljihunka da takardun Naira in za ka je kasuwa siyayya, domin za ka iya shiga kasuwa, manyan kantuna, wuraren cin abinci ko ma kowane irin kanti ka biya kudi da katinka na banki.

Terbia ya ce, “A maimakon ka baiwa mutane tsabar takardun kudi, kana iya yi masu tiransfa kawai, abubuwa masu yawa da a baya kake da bukatan ka yi su da tsabar takardun kudi a yanzun ba ka bukatar yin na su da takardun kudin. Biyan kudi ta manhajar yanar gizo a yanzun yana koran yin amfani da takardun kudin ne.”

Wani kuma dalilin da ya bayar shi ne na rashin karfin takardun kudin namu, a sa’ilin da ma fi girman takardan kudin kasar nan ita ce takardar Naira dubu guda, wacce take kasa da kiman dalar Amurka uku.

“Manyan takardun kudi ne muke ajiye wa a matsayin masu kima, amma yanzun takardan kudi ta Naira ba ta da kimar da za ka iya ajiye ta a matsayin wasu kudade masu kima. Matukar kana son takardun kudade masu kima, tilas ne sai dai ka nemi kudaden waje. In kana son ka yi tsimin kudade masu kima a gidanka, sai dai ka yi tsimin takardar dalar Amurka 50 ko ta 100, ko kuma ka yi tsimin takardar Fam na Ingila 20 ko Fam 50. Ajiyar takardun Naira ya yi rauni kasantuwan ba wasu manyan takardun kudade a cikin su.”

A cewar shi, in har ka ga mutum yana rike da takardan Naira a yanzun, to sai dai yana son ya yi wata karamar siyayya ce kadai.

Ya ce yanzun Naira tana da magauta a wajen yin cinikayya kamar su ATM da su PoS.

“Ta hanyan tura kudi, za ka iya tura akalla har Naira 1,000. Ba ma ka bukatar tsabar kudi domin ka sayi katin kira a wayarka ko ma a ATM, sai dai ka tura kawai,” in ji shi.

Exit mobile version