A yau Lahadi ne aka bude dandalin Liangzhu a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Dandalin karo na hudu, zai mayar da hankali ne ga tattauna batun tarin kalubale, dake tattare da kare gado da hanyoyin zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa.
A shekarar nan ta 2026 ne ake bikin cika shekaru 90 da gano baraguzan Liangzhu. Kuma dandalin na bana na da take “Hade zamanin baya da mai zuwa: Kare gado domin zamaninmu”. Kazalika, dandalin ya hallara jamiai, da masu aikin hako ababen tarihi da malamai daga sassa daban daban na duniya.
Yayin wata ganawa da manema labarai, Zhang Ling, jamia a hukumar lura da gadon aladu ta kasar Sin, ta ce ana sa ran kwararru, da masana za su tattauna game da batutuwa da dama, tun daga wadanda suka jibanci wayewar kai ta zamanin dauri, zuwa bincike game da aikin hako kayan tarihi a tsaffin biranen da suka gushe. A daya hannun kuma, za a baje kolin sabbin sakamakon bincike da ci gaba da aka samu a wannan fage.
A nata tsokacin kuwa, cikin jawabin bude dandalin da ta gabatar, ministar raya aladu ta kasar Girka Lina Mendoni, cewa ta yi ya zama wajibi jamaa su matsa gaba daga dabarun gargajiya, su rungumi masu wanzuwa, kana su rike tsarin gudanarwa mai samar da kariyam game da dukkanin bangarori da nufin kare aladu na gado yadda ya kamata.
A bangarensa kuwa, cikin wani sako ta kafar bidiyo da ya gabatar, mataimakin babban daraktan hukumar UNESCO ta MDD Nayef Al-Fayez, cewa ya yi tsarin gudanar da yawon bude ido mai dorewa, zai taimaka wajen kare aladu na gado ta hanyar kara wayar da kayan jamaa game da muhimmancin gado domin zuriuin masu zuwa, da kyautata fahimtar aladu, da karfafa yanayin rayuwar alummu masu nasaba da hakan”. (Saminu Alhassan)














