Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya ce ayyukan raya ƙasa da kuma abin da ya bayyana a matsayin inganta tsaro na daga cikin dalilan da suka sa Tinubu ya cancanci wa’adin mulki na biyu.
Tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya ce Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya cancanci a sake zaɓensa a 2027, saboda ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta gudanar da kuma ci gaban da ya ce an samu a fannin tsaro.
Pakistan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ayyukan da aka gudanar a Kano, waɗanda ya ce kuɗaɗensu sun haura naira tiriliyan tara.
A cewarsa, irin waɗannan ayyuka da sauran matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na daga cikin hujjojin da ke nuna dalilin da ya sa shugaban ƙasar ya cancanci a sake ba shi dama ya ci gaba da mulki.
Ya kuma yi nuni da abin da ya bayyana a matsayin inganta tsaro, yana mai cewa ya kamata a yi la’akari da matakan da gwamnati ta ɗauka wajen magance matsalolin tsaro yayin tantance ayyukanta.
Pakistan ya bayyana cewa ayyukan raya ƙasa da inganta tsaro na daga cikin muhimman abubuwan da masu zaɓe za su duba yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙaratowa.














