Ministan Ma’aiktar Bunkasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ya yi kira ga kwararrun Likitocin Dabbobi da ke aiki a Rundunar ‘yansanda, da su yi kokari wajen bai wa fannin kiwon dabbobi kariyar da ta kamata.
Maiha, ya bayar da wannan shawarar ce; a taron bita ta wayar da kai na kwana biyu a Abuja da aka shirya, karkashin shirin aikin tallafawa da dogaro da kai na kiwo (L-PRES).Ya yi kira a gare su da su yi amfani da kwarewarsu wajen sanya ido kan dakile yaduwar cututtukan da ke kama dabbobi da yin gangamin wayar da kai kan yi wa dabbobi allurar rigakafin kamuwa da cutuka tare da taimakawa wajen magance rikice-rikice a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Kiran Taron Wakilan Gamayyar Kungiyoyin Masu Aikin Sa Kai Ta Kasar Sin Karo Na 3
- PRP Ta Gargadi Sabon Shugaban PDP Kan Neman Taimakon Kasashen Waje A Rikicin Jam’iyya
Ministan ya jaddada muhimmancin tura kwararrun likitocin dabbobin aikin na ‘yansanda, musamman domin taimakawa wajen kara karfafa kula da lafiyar dabbobi da kuma kara karfafa tsaro “Duba da yadda ake da sama da kwararrun likitocin dabbobin 80 da kuma sauran kwararru sama da 70 a cikin aikin na ‘yansanda a kowace jiha a kasar, gudanmawarku a fannin, na da matukar muhimmanci “.
Kazalika, Mukhtar ya kuma bukaci Babban Shugaba a Cibiyar Kula da Kiwon Lafiyar Dabbobi ta Kasa (CBON), Samuel Anzaku, ya tabbatar da cewa; likitocin dabbobin ‘yansanda, sun shiga cikin aikin gangamin yi wa dabbobi allurar rigakafi gadan-gadan tare da ci gaba da gudanarwa a daukacin fadin kasar nan da kuma kara sanya ido kan dakile yaduwar cututtukan dabbobi da ke shigowa ta iyakokin wannan kasa.
Ita kuwa a nata jawabin, Mataimakiyar Babban Sifoto na ‘yansanda, AIG Aishatu Baju Abubakar, wadda kuma ta wakilce shi a wajen taron, Sifetan ya yaba da irin salon shugabancin ministan tare kuma da yabawa kan yin hadakar a karkashin shirin na L-PRES, inda ya bayyana cewa; hakan zai taimaka wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kara wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Shi kuwa a nasa jawabin, Babban Shugaba a Cibiyar Kula da Kiwon Lafiyar Dabbobi ba Kasa (CBON), Samuel Anzaku ya zayyano irin kokarin da cibiyar ke ci gaba da yi, na dakile yaduuwar cututtukan dabbobi a daukacin fadin kasar. Shi ma a nasa bangaren, a jawabinsa na maraba a madadin jami’in shirin na kasa, Mustapha Mohammad, ya shawarci mahalarta taron da su karara yin aiki da sauran hukumomin gwamnati, domin cimma burin da aka sanya a gaba.














