An  Bukaci Yin Gwajin Kwayoyin Halitta Kafin Aure Don Kare Yaduwar Cutar Sikila

Sikila

Daga Maigari Abdulrahman,

Masana da warkakkun cutar sikila sun bukaci yin gwajin kwayun halitta kafin aure don kare yaduwar cutar sikila, haka sun yi kira kan wayar da kan mutane kan abubuwan da ake yadawa dangane da cutar.

Laákari da yawaitar masu cutar sikila a Najeriya fiye da kowace kasa a duniya, masanan sun nemi makarantu, malaman addini, sarakunan gargajiya da iyayen alúmma da su yi anfani da damar su wurin fadakar da alúmma muhimmancin yin gwajin kafin aure domin rage haifar yara da cutar.

Madam Josephine Olunaike, shugabar kungiyar tallafawa masu cutar sikila kuma wacce ta taba kamuwa da cutar ce ta yi wannan kiran yayen bukin kaddamar da littafi kan waraka daga cutar sikila na Malam Shehu Muhammad mai suna Ï’m a surbibor: the story of my triumph ober sickle cell pains”, a Abuja

Shugabar ta ce, “yana da muhimmanci kowa ya san gwajin kwayun halittarsa domin dakile haifar yara da cutar sikila. Lalle ne a karfafa yin gwajin kafin aure, kada zafin so ya rufe ma masu shirun aure ido, domin idan matsalu su ka yi yawa to soyayyar ma takan dushe ne.”

“Akwai mutanen karkara,suma ya kamata a fadakar da su, ya kamata malaman addini da sarakunan gargajiya su taka muhimmiyar rawa don ganin an shawo kan matsalar,”in  ji ta.

Shugabar, wacce ta ce wasu na da karancin sani kan gwajin ma kansa, yayin da wasu kuma  matsalar kudi ke hana su, ta ce akwai bukatar ganin an samar da hanyoyin yin gwajin kyauta a asibitoci.

A nasa bangare, mawallafin littafin kuma warkakke daga cutar silikar, Mallam Shehu Muhammad, ya ce duk da hadarin da ke tattare da cutar sikila, dayawan mutane ba su fahimci hadarin da ke tattare da illar rashin yin gwajin ga maáurata ba.

Haka kuma, ya koka kan rashin ilimin cutar daga bangaren iyayen da ke fama da cutar da ma su masu kansu masu cutar, ya yi kira kan wayar da kai a kan matakan saukaka zafi ga masu cutar da kular da ya kamata su samu.

A ci gaban jawabinsa, Malam Shehu ya koka kan tsangwamar da masu cutar sikila ke fuskanta, kama tun daga makarantu har zuwa wurin aiki a cikin alúmma, wanda hakan ke raunata su da saka su cikin karin wata damuwa.

A wani taron, ministan lafiya na kasa, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyna cewa, Najeriya ce da mafi yawan masu cutar sikila a duniya, wanda kaso 50 zuwa 80  na  masu dauke da cutar a Najeriya, suna mutuwa ne kafin cika shekara 5 a duniya, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana, in ji shi

Exit mobile version