Mahdi M Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home JAKAR MAGORI

An Cafke Uwa Da Laifin Kulle Danta Tsawon Shekaru 28

by Mahdi M Muhammad
January 6, 2021
in JAKAR MAGORI
2 min read
Kurkuku
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

An kama wata uwa a kasar Sweden bisa zargin kulle danta a cikin gidansu na tsawon shekaru 28, kuma ta bar shi da rashin abinci mai gina jiki wanda ya yi sanadiyyar hana hakorinsa fitowa, in ji ’yan sanda da kafofin yada labarai a ranar Talata.

“Ana zargin mahaifiyar ne da hana ‘yanci kai ba bisa ka’ida ba da kuma haifar da lahani a jikin dan Adam,” in ji kakakin’ yan sanda na Stockholm Ola Osterling a gaban AFP.

samndaads

Ya ce, mutumin ya kasance an kulle shi na tsawon lokaci a cikin gidan da ke kudancin birnin Haninge na Stockholm, amma ba zai ce komai ba game da rahotannin da jaridar Edpressen da Aftonbladet suka bayar cewa an tsare shi na tsawon shekaru 28.

Rahotannin sun ce mahaifiyar ta cire danta daga makaranta tun yana shekara 12 kuma ta garkame shi a cikin gidan tun daga lokacin. Wani dan uwan da ba a bayyana sunansa ba ne ya sami mutumin mai shekaru 41 yanzu a ranar Lahadi bayan an kai mahaifiyarsa, ‘yar shekaru 70, zuwa asibiti, Edpressen ta ruwaito.

Mahaifiyar ta musanta aikata laifin, in ji hukumar shigar da kara ta Sweden.

Likitocin da asibitin suka sanar da ‘yan sanda game da lamarin. ‘yar uwar mahaifiyar da ba a san ta ba wanda ta sami mutumin, ta ce, gidan kamar ba a tsaftace shi cikin shekaru ba. Ya ce, “Akwai fitsari, da datti da kuma kura. Ya ji warin rubewar wani abu. Dole ne ta ratsa ta cikin tarkacen shara don wucewa ta farfajiyoyin, saboda ba bu wanda ya tsabtace gidan tsawon shekaru.”

Ta kara da cewa, “Ina cikin matukar damuwa, amma a lokaci guda na samu salama. Na kasance ina jiran wannan rana tsawon shekaru 20 saboda na gano cewa tana sarrafa rayuwar danta gaba daya, amma ban taba tunanin abin ya kai girman hakan ba. Ina godiya kawai da ya samu taimako kuma zai rayu.”

SendShareTweetShare
Previous Post

Ta Wayi Gari An Bincine Mata Kunne Yayin Yi Mata Tiyatar Hanci

Next Post

An Hana Wani Musulmi Takardar Zama Dan Kasar Jamus Saboda Kin Musabiha Da Mace

RelatedPosts

Uba Ya Hori Kare Don Hana ’Yarsa Amfani Da Waya Yayin Aiki

Uba Ya Hori Kare Don Hana ’Yarsa Amfani Da Waya Yayin Aiki

by Mahdi M Muhammad
11 hours ago
0

Wani mahaifi a kudu maso yammacin kasar Sin ya kirkiro...

Uwa Ta Jefar Da Jaririnta A Kwandon Shara Saboda Ya Yi Kama Da Tsofaffi

Yadda Wani Masifaffen Kare Ya Kusa Halaka Yarinya

by Mahdi M Muhammad
11 hours ago
0

Wani abin bakin ciki ya faru yayin da wata yarinya...

Uwa Ta Jefar Da Jaririnta A Kwandon Shara Saboda Ya Yi Kama Da Tsofaffi

Uwa Ta Jefar Da Jaririnta A Kwandon Shara Saboda Ya Yi Kama Da Tsofaffi

by Mahdi M Muhammad
11 hours ago
0

Wata budurwa ta yi watsi da sabon haihuwarta a cikin...

Next Post
Musulmi

An Hana Wani Musulmi Takardar Zama Dan Kasar Jamus Saboda Kin Musabiha Da Mace

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version