An fara aikin gina tsarin sadarwa da sigina da wutar lantarki na layin dogo dake iya daukar jirgin kasa mai dakon kayan nauyi a hamadar yammacin Aljeriya a ran 2 ga watan nan da muke ciki, wanda ya kasance layin dogo irinsa na farko a hamadar Afirka.
Wannan layin dogo yana da tsawon kilomita 950, kamfanin China Railway Construction Corporation (CRCC) tare da wani kamfanin gwamnati na kasar Aljeriya ne ke gina kilomita 575 na layin. Shi ne babban aikin gine-gine mafi girma da kamfanin Sin ya taba ginawa a Aljeriya.
Tun bayan fara amfani da wannan layi a watan Fabrairun bana, ya inganta tsarin jirgin kasa na kasar Aljeriya, kuma ya taimaka wajen hada lardunan kudu maso yammacin kasar da bunkasa tattalin arzikinsu.
Wannan aikin zai zamanantar da layin dogo a bangaren tsarin zirga-zirga, da tsarin watsa bayanai, da kuma tsarin samar da wutar lantarki, wanda zai ba da tallafi mai karfi ga bunkasa albarkatun ma’adanai da kuma mabambantan nau’ikan tattalin arziki a kasar. (Amina Xu)














