A shekarar 1992 ce Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero ya ba shi muƙami na sarautar Galadiman Kano, muƙamin da ya sa da kuma ƙara ƙara ma sa farin jinin al’umma.
Idan ana magana ne a kan shi marigayi Galadiiman Kano, kamar yadda wani mai ba Gwamnan Kano shawara a harkokin da suka shafi majalisun Sarakuna, Alhaji Tijjani Mailafia Sanka ya ce tsarin da shi marigayin ya yi na hannunsa a buɗe da son jama’a hakan ya ƙara ma sa farin jini daga wurin al’ummarsa.
“Idan dai ana maganar Talakawan sa ne Galadima na iya zuwa ko ina ne ko kuma wane tsawon lokaci za a ɗauka. Duk lokacin da ka gan sa ko ka same shi, za ka gane shi yana ƙoƙari ne na taimaka wa talakawan sa kan matsalolin da suka dame su. Idan ka ga wasiƙa, ko wayar sa duk domin saboda wani ko wasu ne wato talakawa.
Bada daɗewa ba ne wani ritaya Soja wanda yak e fama da matsalolin ido ya je wurin Sarkin Musulmi ya ce daga wurin Galadima ya ke.
“Cikin wani ikon Allah sai na kasance ina can don haka lokacin da aka kira Galadima,sai ya ce bai san ritaya Sojan ba,amma kuma shi Sultan ɗin ya taimaka ma shi idan har yana fama da matsalolin idon kamar yadda ya ce. Ko ya san ka ko bai san ka ba zai taimaka ma ka kamar dai yadda Alhaji Tijjani Mailafia ya ce,”.
Shi ma, a na shi jawabin, shi ma Hakimin Tarauni a Kano, Alhaji Ado Kurawa, ya ce marigayin ya yi rayuwa inda ya yi amfani da yawan shekarun sa yana biyan buƙatun mutane ne wato Talakawa.
Ya tuna da lokacin a shekarar 60 marigayi ya yi amfani da matsayin sa na ɗan majalisar Arewa domin taimakawa al’ummar Jihar sa.
“Zai yi wuya a cike giɓin da mutuwar sa tasa bari saboda shi mutum ne wanda ke son taimakawa al’umma da yi ma kowa fatan alkhairi, ba tare da yana wasu tunanin bambance bambance ba kamar dai yadda mutumin ya bayyana,”.
Kamar yadda ya ce, rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da ta Galadiman Kano, masarautar Kano ta yi rashin manyan mutane masu ƙima da daraja.
“Al’ummar Kano ba za su manata da shekarar ba cikin sauri saboda sheka ce wadda manyan Shugabanni biyu suka mutu.
Ibrahim Ahmad Karaye, wani mataimaki ga marigayi Galadiman Kano, ya bayyana cewa Galadiman a matsayin mutumin mutane ne.
“Yana son taimakawa mutane ba tare da la’akari da irin matsalarsu da mutum ke fuskanta ba, hakan shi yasa mutane suke ƙaunar sa kamar yadda ya bayyana,”.
Wani mai dafawa marigayi Galadiman Kano abinci, da ake kira da suna Malam Abdurrahaman Ahmad, cewa ya yi shekara talatin da biyar yana yi wa marigayin aiki ya kuma ƙaru sosai, saboda kuwa ya koyi abubuwa masu ɗimbin yawa, musamman ma ta ɓangaren da ya shafi hulɗa da jama’a.













