Kamfani Siminti na DANGOTE ya horar da manoma 60 waɗanda suke daga gundumar Okpella, ƙaramar hukumar Etsako ta gabas ta Jihar Edo.
Shugaban kasuwanci na Kamfanin,Sunday Oyelude, shi ne wanda ya bayyana haka ranar Laraba ta makon da ya gabata lokacin rufe taron horarwa na kwana uku na da kuma taimaka wa al’umma domin su tsaya da kansu wanda aka yi wa manoman da ke gundumar.
Da yake jawabi lokacin da ake raba kayan ga waɗanda suka cancanta, Oyelude ya ce lamarin taimakawa manoma yana daga cikin yarjaejeniyar Kamfanin da aka yi domin taimakawa al’ummar da suke gundumomin .
“Tsarin ya kasance ne a ƙarƙashin inuwar yarjejeniyar da aka yi saboda a taimakawa manoman da suke wuraren.
Ya ce “Wannan taimakon da ake yin a kowace shekara inda ake taimakawa da horar da mutane ƴan asalin wuraren akan yadda za ayi amfani da kayan noman da aka rabawa mutanen.
“Ku san mutane 60 ne suka samu horarwa wanda ƙwararre kan lamarin da ya shafi aikin noma wanda aka yi kwana biyu inda aka raba kayan noman ga waɗanda suka samu horarwar kamar yadda Oyelude ya bayyana,’.
Shi ma jami’in kula da jin daɗin ma’aikata na Kamfanin, Daniel Obamina, cewa ya yi taimakawar da aka yi ta bada kayan an yi hakan ne saboda a bunƙasa rayuwar manoman da suke wuraren, bugu da ƙari akwai bunƙasa hanyoyin noma na zamani da yadda ake yin su.
Obamina ya ce an zaɓi manoma 60 ne daga ƙuyuka daban daban daga cikin gundumar ta Okpella.
Ya ce manoman da suka samu horarwa an horar da su ne akan magungunan da ake amfani da su a gona da yadda za ayi amfani da su, yadda za a zuba Taki, kai har ma da yadda za a kula da kayan amfanin gonar da yadda za ayi in an samu cin riba da kuma yin asara.














