A matsayin aikin rufe “bikin nuna fasahar bidiyoyi na kasa da kasa”, an gudanar da bikin dare domin nuna fasahar bidiyoyi na kasa da kasa a cibiyar baje koli ta Shanghai, inda aka fitar da jerin bidiyoyin dake hada fasahar kirkire-kirkire da fasahohi tare a ran 18 ga watan Oktoba.
A gun bikin, an nuna matsakaita da gajerun wasannin kwaikwayo masu nau’ika daban-daban bisa jigogi masu yawa, tare da hada kai da dandamali da dama domin kara ba da karfi, ta yadda ayyuka masu kyau da suka fito daga rayuwa su ci gaba da bayyana a cikin wadannan wasanni.
Shen Haixiong, shugaban CMG ya halarci taron da kuma kaddamar da wannan biki bisa hadin gwiwa da wasu manyan baki. Ban da wannan kuma Shen Haixiong da Zhu Zhongming, mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar JKS na birnin Shanghai, kana magajin birnin, sun gabatar da jawabi bi da bi a yayin taron, kuma sun kaddamar da “aikin hadin gwiwar samar da fasahar bidiyoyi ta kasa da kasa” cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)














