A yau Jumaa ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako ga dandalin tattauna batun jagorancin duniya na Xiongan na shekarar nan ta 2026.
Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce a halin da ake ciki, sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu a karbi ba na gaggauta faruwa a sassan duniya, kana ana ganin fadadar gibi a fannin zaman lafiya, da ci gaba, da tsaro da jagoranci. Ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya, wadda manufarta ita ce ingiza gina karin adalci, da daidaito a tsarin jagorancin duniya, da samar da duniya mai inganci.
Shugaba Xi, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa don aiwatar da akidar jagorancin duniya, mai kunshe da zurfafa shawarwari, da hada hannu wajen samar da gudunmawar cimma moriyar bai daya, da karfafa tafiya bisa kwarin gwiwa, da shawo kan batutuwa masu wahala ta hanyar hadin gwiwa, da ingiza aiwatar da tsarin jagorancin duniya, da shigar da karin tabbaci da kyakkyawan karsashi cikin duniya mai cike da rashin daidaito da sauye-sauye, da hada karfi wajen samar da alumma mai makomar bai daya ga dukkanin biladama.
An kaddamar da dandalin Xiongan na 2026 ne a yau, a sabon yankin Xiongan na lardin Hebei, bisa taken “Sake gina kwarin gwiwa da hadin gwiwa: Sauye-sauye da ba ga irinsu ba cikin karni, da kwaskwarima da inganta tsarin jagorancin duniya”. (Saminu Alhassan)














