Lafiyar jiki ta dogara ne kan kyakkyawar kulawa ta yau da kullum, kuma a ganin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai tarihin sama da shekaru dari daya a duniya, cikakke kuma tsattsauran jagoranci a jam’iyyar, ita ce kyakkyawar kulawar da aka yi mata.
Wannan ba matakin gyara na wucin-gadi ba ne, tsari ne na dogon lokaci domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi ta inganta kanta.Niyyar jam’iyyar ta gyara kanta, ya samo asali ne daga hikimar gargajiya ta kasar Sin.
Ta yin la’akari da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na 20 na JKS da za a gudanar, Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima a kanta, da tunkarar kalubalen da ke tattare da mulki na dogon lokaci, tare da gabatar da “dabarar Sin” a matsayin mafita ga jam’iyyun siyasa a duniya baki daya. (Mai Fassara: Maryam Yang)














