Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran wasanni na Spain sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid na tattaunawa da ɗan wasanta, Jude Bellingham, kan yiwuwar ƙara masa wa’adin kwantiragi har zuwa shekarar 2031.
Bellingham, mai shekaru 23, yana da sauran shekaru biyu da rabi a kwantiraginsa na yanzu da ƙungiyar.
Sai dai mahukuntan Real Madrid na son cimma sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan domin tabbatar da ci gaba da zamansa a Santiago Bernabéu.
Ɗan wasan tsakiyar ya koma Real Madrid daga Borussia Dortmund ta Jamus a shekarar 2023 kan kuɗi Yuro miliyan 88.
Tun bayan komawarsa ƙungiyar, Bellingham ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe manyan kofuna, ciki har da La Liga da gasar Zakarun Turai.
Ya zura ƙwallaye 49 a wasanni 152 da ya buga wa Real Madrid, abin da ya ƙara nuna muhimmancinsa a ƙungiyar.
Rahotannin sun kuma nuna cewa kocin ƙungiyar, José Mourinho, na farin ciki da gudummawar da Bellingham ke bayarwa, inda ake sa ran ƙarin kwantiragin zai ƙara ƙarfafa gwiwar ɗan wasan wajen ci gaba da taka leda a Madrid.














