‘Yan majalisar dokokin kasar Gambiya, sun amince da wasu shawarwari wanda ya haramta yi wa mata kaciya, bayan da aka kada kuri’a a majalisar.
Tun a 2015 ne dai aka haramta yi wa mata kaciya a Gambiya, amma tsarin al’adar da ke da tushe ya ci gaba da yaduwa, kuma hukuncin farko da aka yanke a bara ya haifar da cece-kuce a kan dokar.
- Tsoffin Shugabannin Sin Da Guinea Bissau Sun Taka Rawar Gani Wajen Kirkirar Zumunci Tsakanin Kasashen Biyu
- Gwamnan Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙirƙiro Ayyukan Ci Gaba
Bayan zazzafar muhawara a ranar Litinin, kudirin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin hadin gwiwa na kiwon lafiya da jinsi ya zartas da cikakken zama a majalisar, inda ‘yan majalisa 35 suka kada kuri’ar amincewa da kudurin, yayin da 17 kuma suka ki amincewa, biyu kuma ba su kada kuri’a ba.
A halin yanzu an sanya ranar 24 ga watan Yuli, a mastayin ranar da za a yanke hukuncin ko za a sanya kaciyar nata a matsayin aikata laifi ko akasin haka.
Idan majalisar ta amince da hakan, Gambiya za ta zama kasa ta farko da ta janye dokar hana kaciya.
A watan Maris ne aka yi karatu na biyu inda ‘yan majalisa biyar daga cikin 53 suka kada kuri’ar kin amincewa da shi, daya kuma ya ki kada kuri’a.
Bayan karatu na biyu, kwamitin hadin gwiwa ya gudanar da taron tuntubar al’umma na kasa tare da shugabannin addini da na gargajiya, likitoci, wadanda abin ya shafa, kungiyoyin farar hula da masu kaciya da dai sauransu.
Sakamakon bincike da tuntubar da aka yi na nuni da cewa, duk nau’ikan yi wa mata kaciya cin zarafin mata ne da azabtarwa da kuma nuwawa mata wariya.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce yi wa mata kaciya ba shi da wata fa’ida ga lafiya kuma yana iya haifar da zubar jini da yawa, firgita, matsalolin tunani har ma da mutuwa.