Bankin Stanbic na kasar Kenya, wanda reshe ne na rukunin Standard Bank na kasar Afirka ta Kudu, ya kaddamar da aikin amfani da tsarin biyan kudi da kudin kasar Sin RMB kai tsaye (CIPS), a ranar Juma’a.
A wajen bikin kaddamarwar, jakadiyar kasar Sin a kasar Kenya, Madam Guo Haiyan, ta ce yanayi mai armashi da ake ciki wajen gudanar da hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Kenya ne ya sa ake bukatar kyautata ayyukan biyan kudi, da samar da rance.
Kana yadda ake habaka amfani da tsarin biyan kudi na CIPS a nahiyar Afirka ya nuna niyyar kasar Sin ta karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka a bangaren hada-hadar kudi.
A nasa bangare, Jonathan Muga, babban manajan sashen kula da kamfanoni da bankunan zuba jari na bankin Stanbic na kasar Kenya, ya ce yadda aka kaddamar da aikin amfani da tsarin CIPS wajen biyan kudi da kudin Sin RMB kai tsaye, zai sa kaimi ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Kenya.
A watan Yunin bana, babban bankin kasar Sin, ya sahalewa rukunin Standard Bank, gami da bankin ICBC na kasar Sin, gudanar da aikin biyan kudi da kudin RMB a nahiyar Afirka karkashin hadin gwiwarsu. (Bello Wang)














