An Kama Wasu Bisa Zargin Nuna Wa ‘Yan Wasan Ingila Wariyar Launin Fata

Wariyar Launin Fata

Hukumomi a kasar Ingila sunyi holen wasu mutane masu amfani da kafafen yada labarai na zamani wadanda ake zargi da zagin ‘yan wasan tawagar kasar Ingila da suka hada da Bukayo Saka Da Jadon Sancho da Marcus Rashford bayan sun kasa ciwa Ingila bugun fanareti a wasan karshe na Euro 2020 da sukayi rashin nasara a hannun kasar Italiya

A ranar Juma’a ne dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Bukayo Saka ya ce daman ya san za a ci zarafinsa tun da ya kasa ci wa tawagar Ingila fenareti ranar Lahadin satin daya wuce  a filin wasa na Wembley  a gasar Euro 2020.

Dan wasa Saka, wanda ya kasa cin fenaretin karshe da Marcus Rashford da Jadon Sancho da suka fara zubar da nasu, ya bai wa kasar Italiya damar nasara a kan Ingila a gasar bana kuma ‘yan  wasan uku sun yi ta samun sakonnin cin zarafi a kafar sada zumunta tun daga ranar Lahadi.

Saka ya bayyana a shafinsa na Twitter cewar ba zai bari kalaman batancin da ake ta yi masa su rage masa karsashi ba saboda haka zai ci gaba da buga wasanninsa ba tare da gwiwarsa tayi sanyi ba.

Kawo yanzu ana tsare da mutum biyar kan zargin tura sakonnin kalaman cin zarafi ga bakaken ‘yan wasan na Ingila ukun da suka kasa cin fenariti ranar Lahadi a filin wasa na Wembley.

Kuma fira ministan kasar, Boris Johnson ya bayyana cewa dole ne a hukunta wadanda sukayi amfani da shafukan nasu wajen cin mutuncin matasan ‘yan wasan domin kada a sake samun irin wannan matsalar a nan gaba.

Tawagar ‘yan wasan kasar Italiya ce ta yi nasara a kan Ingila da ci 3-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 a gasar ta Euro 2020 sannan wannen ne karo na farko da Italiya ta lashe gasar tun bayan wanda ta lashe a shekara 1968, ita kuwa Ingila karon farko da ta kai wasan karshe a babbar gasa tun bayan lashe kofin duniya a shekarar 1966, kimanin shekara 55 kenan.

Mutane da dama ciki har da Firaministan Birtaniya, Boris Johnson sunyi fatali da kalaman wariyar da aka yiwa ‘yan wasan biyo bayan gaza lashe kofin gasar Euro 2020 da aka buga wasan karshe a ranar Lahadin data gabata.

A cewar Johnson daga yanzu za a rika daukar mataki a kan wadanda suka ci zarafin dan wasa da kalaman wariyar launin fata ta kafar internet kamar yadda aka gani a ranar Lahadi kuma gwamnati ba zata saurarawa duk wanda aka kama ba.

Sannan ya tabbatar da cewa majalisar Burtaniya zata tattauna akan yadda za’a hukunta duka kamfanonin sada zumuntar idan har suka gaza daukar matakai akan masu zagin mutane a shafukan nasu saboda a cewarsa suna da hanyar da zasu iya hana hakan.

 

 

Exit mobile version