An rantsar da zababben Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Kudu-maso-Yamma, Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa na 13 da safiyar Talata.
An rantsar da shi da misalin karfe 9:40 na safe.
- Da Dumi-Dumi: Akpabio Ya Lashe Zaben Shugaban Majalisar Dattawa
- Tinubu Bai Bude Iyakokin Nijeriya Ba -Kwastam
Tsohon Gwamnan Akwa Ibom ya doke zababben Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdul’aziz Yari a zaben Shugaban Majalisar Dattawa ta 10.
Akpabio ya samu kuri’u 63 daga cikin kuri’u 109 da aka kada, yayin da Sanata Yari, wanda ya zama Sanata a karon farko, ya samu kuri’u 46.
An dai samu sabani kan batun nadin Yari, amma aka yi watsi da shi a kan cewa shi tsohon dan majalisar wakilai ne kuma dokar majalisar dattawa ta amince masa ya tsaya takara.
Tun da farko, zababben Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya zabi Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Zababben Sanata mai wakiltar Ogun ta Yamma, Solomon Adeola ne ya goyi bayan nadin.
Haka kuma, zababben Sanatan Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo, shi ne ya tsayar da Abdulazeez Yari, sannan kuma zababben Sanata Jimoh Ibrahim ya goyi bayan Yari.
Sai dai magatakardar Majalisar (CNA), Magaji Tambuwal, ya yi fatali da korafin Tahir Monguno, inda ya bayyana cewa dokar ta bai wa tsohon dan majalisar wakilai da aka zaba a majalisar dattawa.
Daga nan ne CNA ya ayyana rufe nade-naden kuma aka fara kada kuri’a tare da bayyana sakamakon zaben daga baya.
Kimanin gwamnoni hudu na APC da PDP ne aka tura su marawa Akpabio baya.
Gwamnonin Hope Uzodimma na jihar Imo, Seyi Makinde na jihar Oyo da Yahaya Bello na jihar Kogi, da dai sauransu, sun halarci zaben domin kaddamar da majalisar dattawa ta 10.