An Sake Dawo Da ’Yan Nijeriya 116 Daga Libiya

Dawo da ‘yan Nijeriya daga kasar Libya, yana cikin shirin gwamnati na ceto ‘yan Nijeriyan da suka sagale daga kasar ta Libya, ta hanyar hadin gwiwa da kungiyar da ke lura da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM), kungiyar kasashen Turai (EU), da kuma gwamnatin kasar nan.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta tarbi wasu karin ‘yan gudun hijirar da aka dawo da su, tare da wasu jami’an gwamnatin tarayya a sashen sauke kaya na filin saukan Jiragen sama na Murtala Muhammad, da ke Legas.
‘Yan gudun hijirar da aka dawo da su a wannan karon sun kunshi mata 53 da maza 63, da suka hada da manyan mata 46 da yara mata 2 gami da kananan yara maza 5 da maza manya 56, jarirai shida.
Sun iso ne a cikin wani Jirgin saman shata na, Al Burak Airlines, mai lamba, UZ 489, da misalin karfe 12:40 na safiyar ranar Laraba.
Da yake karban wadanda suka yanke wa kansu shawarar komowan, wadanda a baya sun yi nufin shiga kasashen Turai ne ta kasar ta Libya, Mataimakin shugaban hukumar ta NEMA, a shiyyar kudu maso yammacin kasar nan, Mista Segun Afolayan, ya shawarce su da su gargadi masu nufin yin kaura irin nasu.
Afolayan ya ce, yin hijira halas ne ga kowa, amma in mutum ya tsiri yin hijiran ba ta hanyar da ta halasta ba, a bisa sabawa dokokin wasu kasashen, ba abin da kasar da ya tsinci kansa a cikinta za ta yi da ya wuce ta kama shi ta kuma hukunta shi da dokokin kasar ta.
Domin kawo karshen masu yunkurin irin wannan hijirar ta barauniyar hanya, mukaddashin shugaban hukumar na wannan shiyyar, ya shawarci duk mai son yin hijiran da ya ziyarci cibiyar ‘yan gudun hijira da, Migrant Resource Centre opened by IOM, ta bude a bisa hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Rassan cibiyar suna nan a harabobin Ma’aikatar Kwadago da samar da ayyukan yi da ke garuruwan, Benin, Lagos da Abuja.
Ya ce, “Cibiyoyin a bude suke ga dukkanin ‘yan Nijeriya masu nufin yin kaura zuwa wajen kasar nan. A can za su sami bayanan da za su taimaka masu na kasashen da suke da nufin zuwa.”

Exit mobile version