Connect with us

KASUWANCI

An Samu Hauhawar Farashin Kayayyakin Masarufi A Nijeriya

Published

on

A makon da ya gabata ne Hukumar kula da harkokin kididdiga ta kasa ta fitar da yadda farashi yake yadda a kan yadda farashin kayayyaki ya shafi arziki, abin ya tashi daga kashi 11 .14 a watan Yuli zuwa kashi 11. 23 a watan Agusta.

Ita hukumar a cikin rahoton nata wanda aka rarraba ma wakillankafafen watsa labarai ya nua cewar, wannan shi ne lokaci na farko da, wanda daga wannan shekara zuwa waccan na karuwar farashi, wannan kuma ya biyo bayan koma bayan da aka samu har sau goma sha takwas a bangaren karuwar farashin kayayyaki.

Rahoton ya kara bayyana cewar “Yadda ake samun karuwar farashin kayayyaki wadanda ake amfani dasu, abin ya karu da kashi 11.23 ( na shekara zuwa shekara) a watan Agusta na shekarar 2018.

Wannan ya nuna kashi 0.09 na karuwa fiye da wanda aka samu cikin watan Yuli 2018, ( kashi 11.14) wannan kuma shi yake nuna yadda shekara zuwa shekara a ka samu karuwar farshin kayayyaki saboda samun karuwar farashin har sau goma sha takwas.

“An samu karuwar ne a dukkan bangarorin, wannan kuma ya kunshi na wata zuwata ne abin ya karu ne da kashi 1.5 a watan Agusta na 2018, abin ya yi kasa da kashi 0.8 idan aka yi la’akari  akan wanda aka samu cikn watan Yuli na 2018 wato (kashi 1.13).

Hukumar kula da kididdiga ta kasa ya lura da cewar an samu karuwar farashin kayayyaki da kashi 11.67, na shekara zuwa shekara, a watan Agusta 2018 daga kashi 11.66 wanda aka yi cikin watan Yuli, yayin da kuma karuwar farashin kayayyaki na kauyuka ya karu da kashi 10.84 a watan Agusta daga kashi 10.83 a watan Yuli.

Shi kuma na wata zuwa wata ita hukuma kula da kididdigar ta kasa ta nuna cewar ala’amari karuwar farashin kayayyaki na birni abin ya karu da kashi daya a watan Agusta, abin kuma ya yi kasa da kashi 0. 23 daga kashi 1,2, 3 wanda aka samu cikin watan Yuli, ya yin da kuma shi al’amarin na kauye ya karu da o.96 a watan Agusta, abin ya yi kasa da kashi 0.22 daga kashi 1.18 wanda aka samu a watan Yuli na 2018.

 
Advertisement

labarai