An tsinci gawar jarumin fina-finan Nollywood, Prince Abuchi Ikpo a gidansa da ke Asaba a jihar Delta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Talata.
- Na Yi Takaicin Zama Ministan Matasa Da Wasanni A Gwamnatin Buhari —Solomon Dalung
- Da Wuya A Ga Cikar Burin ‘Yan Siyasar Japan Na Yi Wa Kundin Tsarin Mulki Garambawul
Edafe ya ce an kashe jarumin ne a gidansa kuma aka kulle shi har sai da aka gano gawarsa.
“An tsinci gawar a gidansa da ke kusa da unguwar Jesus Save, Asaba, a ranar Litinin.
“Sun kashe shi kuma suka kulle gawar a cikin gidan.
“Babu cikakkun bayanai tukuna,” in ji kakakin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp