Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi da gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar sun samu karramawa a bisa kokarinsu na bunkasa muhalli tare da kare lafiyar muhalli baki daya a fadin Nijeriya.
An karrama sune a garin Abuja jiya a yayin bude taron kungiyar masu kula da gandun daji ta kasa ‘Enbironmental Health Officers Registration Council of Nigeria (EHORECON)’.
Wadanda aka karrama matsayin Ambasada sun hada da Ministan Babban biurnin tarayya, Mallam Mohammed Musa Bello da Ministan muhalli, Mallam Ibrahim Usman Jibril da Ministan lafiya, Dakta Isaac Adewole da kuma Dakta Olugbenga Olumida sai kuma babban ragistran kungiyar, Dakta Dominic Abonyi.
Haka kuma an karrama gwamnonin Nasarawa da na Katsina, Tanko Al-makura da Alhaji Aminu Bello Masari da mukamin Ambasadan lafiyar gandun daji.
Haka kuma an karrama Sanata dakta Dalhatu Sarki Tafida da Mista Augustine Ebisille a kan gudummawarsu game da lafiyar gandun daji.
Da yakr jawabin godiya, gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya mika godiyarsa ga kungiyar EHORECON a bisa wannan karramawar da aka yi musu, ya ce, lallai wannan karramawar za ta kara karfafa musu a kan aikin da suke yin a kare muhalli gaba daya.
Ya kuma lura da cewa, tuni jihar bauchi ta yi wa sauran birane zarra a kan matsayin da aka tsara a Abuja na water kashi 15 na kasafin kudi don bunkasa harkar lafiyar gandun daji, kamar kuma yadda kungiyar African Union ta amince.
Shi ma da ya ke karbar karramawar, gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-makura ya lura da cewa, jihar Nasarawa ta shirya kara bunkasa harkokin makarantar kula da muhalli ta ‘School of Enbironmental Health.
A nasa jawabin, Ragistaran hukumar, Dakta Dominic Abonyi ya ce, hukumar ta yi wani shiri na musamman don lura da yadda hukumomi da gwamnatoci ke bayar da hankali ga harkar da ya shafi muhalli.