An yanke wa wasu ‘yan kasar China biyu Meng Wei Kun da Mista Xu Kuai hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari kan kowanne daga cikin laifi biyu da suka hada da hada baki da halasta kudaden haram da kuma yunkurin karbar cin hancin Naira miliyan 50 da Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), ta yi a Sakkwato.
Kowanne daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin zai shafe shekaru shida a gidan yari.
- Mutum 14 Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano Kan Aikata Fashi Da Makami
- Ba Zan Tsoma Baki A Gwamnatin Abba Ba –Kwankwaso
Hukuncin ya biyo bayan daukaka karar da EFCC ta shigar ne a kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta Sakkwato ta yanke, wadda tun farko ta sallami wadanda ake zargin tare da wanke wadanda ake zargin daga tuhume-tuhumen guda uku.
Da yake yanke hukuncin na bai daya a ranar Juma’a, Mai shari’a Abubakar Mahmud Talba na kotun daukaka kara da ke Sakkwato, ya caccaki wadanda ake kara kan kokarin da suke yi na dakile karar.
Ya kuma jaddada cewa dole ne kotuna su bari a saurari kararrakin da ke gaban su.
Mai shari’a Talba ya ci gaba da bayanin cewa hukumar EFCC ta tabbatar da tuhumar daya da biyu daga cikin tuhume-tuhumen uku a gaban babbar kotun tarayya ba tare da wata tantama ba amma ta amince da karamar kotun a kan tuhume-tuhume uku da ake musu.
A cewar Mai Shari’a Talba, “Wadanda ake kara ana tuhumar su ne da laifin hada baki da kuma biyan kudi fiye da yadda dokar hana safarar kudi ta shekarar 2011 ta tanadar.
“Amma abin mamaki, alkalin da ke shari’ar ya yi watsi da hukuncin da ya yanke kuma ya janye.”
Yayin da ya ci gaba da daukaka karar tana da matukar fa’ida, saboda haka alkalin kotun daukaka karar ya yanke wa ‘yan kasar China hukuncin daurin shekaru uku kan kowane daga cikin laifuka biyu tare da zabin tarar Naira miliyan 10 kowane.